Gwamnatin tarayya ba za ta haramtawa manema labarai damar gudanar da aikin su ba - Ministan Al'adu

Gwamnatin tarayya ba za ta haramtawa manema labarai damar gudanar da aikin su ba - Ministan Al'adu

Ministan labarai da al'adu na kasa, Alhaji Lai Muhammad, ya yi sharhi gami da tsokaci kan dambarwar mamayar da dakarun sojin kasa suka aiwatar a kamfanin jaridar Daily Trust reshen jihar Borno tare da yashe wasu ma'aikatun su.

Alhaji Lai Muhammad ya ce, gwamnatin tarayya ba ta da nufi ko wani yunkuri na haramtawa manema labarai 'yancin su na gudanar da aiki illa iyaka gargadi da kuma jan kunne na sanin iyakarsu musamman wajen yada rahotanni kan aukuwar ta'addanci a kasar nan.

Ministan na al'adu ya yi wannan furuci yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Maiduguri, dangane da mamayar da dakarun sojin kasa na Najeriya suka kai ofisoshin jaridar Daily Trust sakamakon yada rahotanni ma su barazana ga tsaro na kasa.

Gwamnatin tarayya ba za ta haramtawa manema labarai damar gudanar da aikin su ba - Ministan Al'adu

Gwamnatin tarayya ba za ta haramtawa manema labarai damar gudanar da aikin su ba - Ministan Al'adu
Source: Depositphotos

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Ministan ya ce dakarun sojin Najeriya sun kai mamaya kamfanin jaridar Daily Trust da ke birnin Maiduguri da kuma na Abuja sakamakon fidda wasu rahotanni ma su barazana ta jefa dakarun sojin cikin hatsari.

KARANTA KUMA: Cikin Bidiyo: Yadda Gwamnan Borno ya fashe da kuka yayin ganawa da Buhari kan ta'addancin Boko Haram

Muhammad ya bayar da tabbacin yadda za a shawo kan wannan lamari gami da magance shi ta hanyar fuskantar juna da kuma sulhu, a yayin da ya yi Allah wadai dangane da yadda 'yan adawa suka harzuka lamarin ta fuskar siyasa.

A yayin tunatarwa kan nuna kwarewa bisa aiki, kazalika Ministan ya nemi manema labarai kan sanin iyakokin su tare da neman su da fahimtar ababe da suka shafi tsaro na kasa musamman a wannan lokuta da yanayi na tsaro a Najeriya ya kai intaha.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel