Yanzu-yanzu: Daga karshe, hukumar Soji ta saki dan jaridan Daily Trust

Yanzu-yanzu: Daga karshe, hukumar Soji ta saki dan jaridan Daily Trust

Bayan kwanaki uku da tsareshi, hukumar sojin Najeriya ta sake dan jaridan Daily Trust, Uthman Abubakar, a birnin jihar Borno, Maiduguri.

Babban editan jaridar Daily Trust, Mannir Dan-Ali, ya sanar da hakan ne bayan ya tattauna da editan wanda wani jami'in soja wanda aka sakaye sunansa ya mayar da shi ofishinsu dake Maiduguri.

Uthman wanda ya jaddada cewa Sojojin basu ci mutuncinsa ba, ya bayyana cewa wayar hannunsa da kwamfutansa na wajen Sojin. Sun fada masa cewa suna bukatan lokaci domin kammala bincike kansu.

KU KARANTA: Yan takaran gwamna 11 sun koma jam'iyyar APC

Mun kawo muku rahoton cewa a ranan Lahadi, ne dakarun sojin Najeriya dauke da bindigu suka yi dirar mikiya a ofishin jaridar Daily Trust dake garin Maiduguri, jihar Borno, tare da yin awon gaba da Editan jaridar, Uthman Abubakar, da wani ma'aikaci, Ibrahim Sawab.

Duk da rundunar sojin bata bayar da wani dalili na aikata hakan ba, jaridar ta ce faruwar hakan ba zai rasa nasaba da wani rahoto da ta buga a yau, Lahadi, ba a kan ofireshon din rundunar soji a yankin arewa maso gabas ba.

Daily Trust ta ce dakarun sojin sun rufe ofishin jaridar na Maiduguri bayan sun kama Editan da ma'aikacinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel