NDLEA ta yiwa sabbin kwamishinonin Kano gwajin kwayoyi

NDLEA ta yiwa sabbin kwamishinonin Kano gwajin kwayoyi

Hukumar hana sha, fatauci da tu'ammali da miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Kano ta gudanar da gwajin kwayoyi ga sabbin kwamishinoni 4 da gwamna Dakta Umar Abdullahi ya nada.

NDLEA ta ce tana tattauna wa da gwamnatin Kano domin ganin an gudanar da gwajin ga duk masu rike da mukaman siyasa a jihar.

Dakta Ibrahim Abdul, shugaban hukumar NDLEA a jihar Kano, ne ya sanar da hakan yayin jawabi ga manema labarai a ofishinsa.

NDLEA ta yiwa sabbin kwamishinonin Kano gwajin kwayoyi

NDLEA ta yiwa sabbin kwamishinonin Kano gwajin kwayoyi
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kwamishinoni 6 na gwamnan APC sunyi murabus

Sabbin Kwamishinonin da aka gudanar da gwajin a kansu su ne; Malam Bashir Yahaya Karaye, Alhaji Mukhtar Ishaq Yakasai, Alhaji Shehu Kura da Alhaji Muhammad Tahir da aka fi sani da 'Baba Impossible'.

"Kwanan nan muka gudanar da gwajin kwayoyi ga sabbin kwamishinoni 4 da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya nada.

"Tuni da ma mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kaddamar da dokar yin gwajin kwayoyi ga duk wanda zai nada a sabon mukami," a cewar kwamandan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel