Karancin albashi: Shehu Sani ya taya yan kwadago zanga zanga

Karancin albashi: Shehu Sani ya taya yan kwadago zanga zanga

Fitaccen dan rajin kare hakkin bil adama kuma dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya afka cikin zanga zangar da yayan kungiyar kwadago suka shirya a babban birnin tarayya Abuja don ganin gwamnati ta tashi tsaye akan sabon tsarin karancin albashi.

A ranar Talata, 8 ga watan Janairu ne dukkanin rassan kungiyoyin kwadago dake jihohin Najeriya gaba daya suka gudanar da zanga zangar lumana domin nuna bacin ransu da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke sakwa sakwa da muradin karancin albashi na N30,000.

KU KARANTA: Jirgin kasan Kaduna-Abuja ya samar da N960,000,000 ga gwamnatin Najeriya

Karancin albashi: Shehu Sani ya taya yan kwadago zanga zanga

Shehu Sani
Source: Facebook

Kungiyar kwadago, NLC, ta nemi shugaba Buhari yayi gaggawar mika ma majalisun dokokin Najeriya kudurin dokar sabon tsarin karancin albashin domin su yi aikin daya kamata akansa kafin ya zama doka, amma suka ce sun fahimci Buhari na kan kafa kan batun.

Da wannan ne kungiyar tayi barazanar idan har Buhari ya sake bai mika ma majalisun dokokin Najeriya kudurin dokar kafin lokacin zaben 2019 yayi ba, tabbas zasu kaurace ma zaben gaba daya, kuma a cewarsu ma’aikata na da ikon zaben wanda suke so ya mulkesu.

Karancin albashi: Shehu Sani ya taya yan kwadago zanga zanga

Shehu
Source: Facebook

NLC na nufin babu ma’aikacin da zai kada kuri’a a yayin zabukan shekarar 2019 kenan, kamar yadda shugaban NLC reshen jahar Edo, Emmanuel Ademokun ya bayyana a ranar Talata 8 ga watan Janairu.

Legit.com ta ruwaito shi yana cewa “Ma’aikatan Najeriya ne suke karbar albashi mafi karanci a duniya gaba daya, don kodai a tabbatar da karancin albashi zuwa N30,000 gabanin lokacin zaben 2019, ko kuma mu kaurace ma zaben gaba daya.”

Sai dai a nasa jawabin, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ya halarci zanga zangar ne domin nuna ana tare da kungiyar kwadago da kuma gwagwarmayar da suke yi, inda yace lamarin ya zame masa al’ada, kuma akida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel