Ka ajiye kudi akan tebur tare da Buhari a daki, za ka ga kudinka idan ka dawo - Tinubu

Ka ajiye kudi akan tebur tare da Buhari a daki, za ka ga kudinka idan ka dawo - Tinubu

- Babban jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa Buhari mutun ne ma aminci da gaskiyar

- Tinubu ya yi jayayyar cewa halayyar manyan yan takarar da ke kan gaba a zabe mai zuwa wato Shugaba Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar basu yi kama ba ta ko ina

- Yace dan mutum ya ajiye kudi akan tebur tare da Buhari a dak zai dawo ya ga kudinsa a wajen da ya ajiye

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa aminci da gaskiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari shine abunda yasa ya zamo dan takarar da ba za a iya kayar da shi ba a zabe 2019.

Tinubu ya yi jayayyar cewa halayyar manyan yan takarar da ke kan gaba a zabe mai zuwa wato Shugaba Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar basu yi kama ba ta ko ina.

Ka ajiye kudi akan tebur tare da Buhari a daki, za ka ga kudinka idan ka dawo - Tinubu

Ka ajiye kudi akan tebur tare da Buhari a daki, za ka ga kudinka idan ka dawo - Tinubu
Source: Facebook

“Shugaba Buhari mutum ne tsayayye kuma mai gaskiya. Ka bar wani Naira akan tebur tare da Buhari a daki. Za ka tarar da Nairan aka teburin dan ka dawo.

“Idan Buhari yace eh ko a’a, toh ka san inda ya tsaya. Duk abunda ya fada har zuciyarsa take.

KU KARANTA KUMA: An ja daga a birnin Shehu yayinda APC ke kokarin tsige Tambuwal

“Ga Atiku, labari ya sha bambam. Hakan yanuna cewa bashi da wani hangen gaba ma kasar sai dai kawai son mulki domin yayi yadda yake so da abubuwa,” inji Tinubu.

Da yake jawabi a Lagas a ranar Talata, 8 ga watan Janairu ta jami’in labaransa, tsohon gwamnan ya ba shugaba Buhari tabbacin cewa ya amshi aikin da ya bashi na kamfen dins da hannu bibbiyu kuma zai yi aiki don kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel