Boko Haram sun sake tafka wani sabon ta'addanci a Borno

Boko Haram sun sake tafka wani sabon ta'addanci a Borno

'Yan ta'addar kungiyar Boko Haram sun sake hari a garin Sajeri da ke jihar Borno inda suka kashe wani malamin addinin musulunci da wani mutum. Sun kuma kone gidajen al'umma da tare da sace kayayakinsu.

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe a kalla mutane biyu tare da kone gidaje takwas a wani sabuwar hari da suka kai a garin Sajeri da ke kusa da Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Premium Times ta ruwaito cewa sun kai harin ne sa'o'i kadan bayan wani harin da aka kai a garin Auno da ke kilomita 25 daga Maiduguri.

Garuruwan Auno da Sajeri duk suna kan hanyan Kano zuwa Maiduguri ne.

Boko Haram sun sake tafka wani sabon ta'addanci a Borno

Boko Haram sun sake tafka wani sabon ta'addanci a Borno
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kwamishinoni 6 na gwamnan APC sunyi murabus

Mazauna garin Sajeri sun ce 'yan ta'addan sun kai farmaki garin ne misalin karfe 10 na dare.

A cewar wasu mazauna garin da suka gudu cikin daji suka kwana, sun ce 'yan ta'addan sun sace musu kayayakin masarufi sannan suka bankawa gidajensu wuta.

"A fusace suka zo, kuma suna da yawa sosai, sun taho da bindigu da adduna," inji wani mazaunin garin mai suna Mustapha Ali.

"Sun harbe wani malamin addinin musulunci da yaki basu kudi. Sun kuma file kan wani mutum kusa da gidansa.

"Sun kuma kwakwulewa wani mutum idanunsa," inji shi.

Kwamandan Operation Lafiya Dole, Benson Akinroluyo ya tabbatar da harin a ranar Litinin yayin hirar da ya yi da manema labarai.

Ya ce zai tafi Auno domin ya ganewa idanunsa halin da suke ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel