Cikin Bidiyo: Yadda Gwamnan Borno ya fashe da kuka yayin ganawa da Buhari kan ta'addancin Boko Haram

Cikin Bidiyo: Yadda Gwamnan Borno ya fashe da kuka yayin ganawa da Buhari kan ta'addancin Boko Haram

A jiya Litinin mun kawo muku rahoton yadda gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya tsinke da hawaye yayin da ya jagoranci tawagar dattawan jihar sa wajen ziyartar shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa ta Villa da ke Abuja.

Majiyar rahoton ta Channels TV da ta hadar har da bidiyon wannan sanarwa ta bayyana cewa, gwamna ya zubar da hawayen sa sakamakon ta'azzarar tayar da kayar baya na ta'addancin Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya musamman cikin jihar Borno.

Sai dai gwamnan ya kyautata zaton sa da cewa, har ila yau al'ummar jihar Borno ba su fidda rai da Buhari ba kan dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ya kasance daya daga cikin ababe da suka shahara a kai.

Ga Bidiyon yadda Gwamna Kashim ya sharbi kuka kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta yada

KARANTA KUMA: Ka da ka tsawaita wa'adin sufeto janar na 'yan sanda - Wani Lauyan Kano ya gargadi Buhari

Cikin zubar hawaye na neman tsayuwar daka ta gwamnati, gwamna Kashim ya mika kokon barar sa ga shugaban kasa Buhari sakamakon koma bayan da aka samu ta fuskar yakar ta'addanci a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Tawagar gwamnatin tarayya da ta halarci taron na ganawa ta hadar da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa; Abba Kyari, shugabannin hukumomin tsaro na DSS da NIA, Shugaban hafsin dakarun tsaro; Abayomi Gabriel Olanisakin da wasu mambobi na majalisar tarayya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel