Rikici ya barke a wurin kamfen din APC a Legas

Rikici ya barke a wurin kamfen din APC a Legas

Kazamin rikici ya barke a wurin kaddamar da yakin neman zaben jam'iyyar APC a jihar Legas yayin da ake tsaka da gabatar da taron.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar wasu 'yan ta'adda da ake zargin mambobin kungiyar direbobin mota (NURTW) ne suka kaure da rikici a wurin taron.

Barkewar rikicin ya jefa jama'ar dake wurin taron cikin firgici tare da gudun neman maboya bayan masu rigimar sun fara harbe-harbe.

Rikici ya barke a wurin kamfen din APC a Legas

Rikici ya barke a wurin kamfen din APC a Legas
Source: Facebook

Rikici ya barke a wurin kamfen din APC a Legas

Rikici ya barke a wurin kamfen din APC a Legas
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Sunaye: Manyan jaruman Kannywood dake cikin kwamitin kamfen din Aisha

Da kyar jami'an tsaro dake wurin suka iya shawo kan lamarin.

Rikicin ya fara ne a daidai lokacin da gwamna Ambode ke gabatar da jawabi, lamarin da ya saka jami'an tsaron dake kula da lafiyar sa fita da shi da mataimakiyar sa, Idiat Adebule, daga wurin taron.

Wasu 'yan jarida biyu da mutane da dama sun samu raunuka sakamakon rikicin.

Wakilin NAN dake wurin a lokacin da rikicin ya barke ya ce ba zai iya tabbatar da an samu asarar rai ba yayin rikicin.

Sakamakon rudanin, mutane da yawa sun rasa wayoyin salularsu da kudade da wasu ababe masu muhimmanci saboda masu yankar aljihu da sauran bata gari da suka hallarci wurin.

NAN ta ruwaito cewa mutane da dama sun taka da kafa ne zuwa gidajensu sakamakon cinkosun ababen hawa da rikicin ya haifar a unguwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel