Da duminsa: Buhari zai gabatar da kudurin dokar sabunta albashi ga majalisar tarayya

Da duminsa: Buhari zai gabatar da kudurin dokar sabunta albashi ga majalisar tarayya

- Daga karshe gwamnatin tarayya ta sanya ranar gabatar wa majalisar tarayya sabuwar dokar da zata sabunta albashin mafi karanci na ma'aikata

Wannan yunkurin zai dakatar da kudurin kungiyoyin kwadago na shiga yajin aiki, wata daya gabanin zaben 2019

- A ranar Talata, gamnatin tarayyar ta amince da turawa majalisar wakilai dokar sabunta albashi mafi karancin a ranar 23 ga watan Janairu

Daga karshe gwamnatin tarayya ta sanya ranar gabatar wa majalisar tarayya sabuwar dokar da zata sabunta albashin mafi karanci na ma'aikata, yunkurin da zai dakatar da kudurin kungiyoyin kwadago na shiga yajin aiki, wata daya gabanin zaben 2019.

Gwamnatin tarayyar ta kafe akan kudurin kungiyar kwadagon akan sabon albashi mafi karancin, inda taki amincewa da bukatar kungiyar akan mayar da mafi karancin albashin zuwa N30,000, kamar yadda kwamitin sulhun shugaban kasar ya gabatar.

Duk da haka, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da tabbacin cewa zai waiwayi wannan bukata tare da sake turawa majalisar tarayya dokar sabunta albashi mafi karancin.

KARANTA WANNAN: Maganar gaskiya: Ni ban umurci EFCC ta daina tuhumar Akpabio ba - Buhari

Da duminsa: Buhari ya sanya ranar gabatarwa majalisar tarayya dokar sabunta albashi

Da duminsa: Buhari ya sanya ranar gabatarwa majalisar tarayya dokar sabunta albashi
Source: UGC

La'akari da yunkurin kungiyoyin kwadago na barazanar shiga yajin aikin kasa baki daya, a ranar Talata, gamnatin tarayyar ta amince da turawa majalisar wakilai dokar sabunta albashi mafi karancin a ranar 23 ga watan Janairu.

Wannan mataki ya biyo bayan kwanaki uku da tattaunawar gwamnatin tarayyar da kungiyoyin kwadagon.

Kungiyoyin kwadago sun amince da wannan rana da gwamnatin ta sanya, amma tayi gargadi akan matakin da zata dauka ma damar gwamnatin ta karya wannan alkawari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel