Buhari ya yarda cewa an samu koma-baya a yaki da Boko Haram

Buhari ya yarda cewa an samu koma-baya a yaki da Boko Haram

- Shugaba Buhari ya amince da cewa ana samun koma-baya a fafutukar kakkabe mayakan Boko Haram musamman a yankin arewa maso gabashin kasar

- Buhari ya amince cewa, sojojin kasar na fuskantar matsin lamba daga mayakan na Boko Haram da ke amfani da salon yakin sunkuru

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da cewa ana samun koma-baya a fafutukar kakkabe mayakan Boko Haram musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.

A yayin wata hirarsa da aka watsa ta kafar talabijin ta Arise a cikin daren ranar Litinin, shugaba Buhari ya amince cewa, sojojin kasar na fuskantar matsin lamba daga mayakan na Boko Haram da ke amfani da salon yakin sunkuru.

Buhari ya yarda cewa an samu koma-baya a yaki da Boko Haram

Buhari ya yarda cewa an samu koma-baya a yaki da Boko Haram
Source: Depositphotos

Shugaban ya kuma amince cewa, sojojin kasar na fama da matsalar rashin karfafa musu guiwa a fagen-daga, amma ya ce, suna kan kokarin shawo kan wannan matsalar.

“Akwai abin da zan kira gajiyawar yaki” in jin Buhari wanda ya kara da cewa, sake bai wa sojojin horo zai magance dabarun mayakan masu ikirarin jihadi.

KU KARANTA KUMA: Bana tsoron Sufeto Janar na yan sanda, zan dauki mataki – Buhari

Sojojin da ke fagen-daga sun sha korafi kan cewa, mayakan na Boko Haram sun mallaki makaman da suka zarce nasu, ku

ma ba sa samun kwarin guiwa yadda ya kamata a cewarsu.

A bangare guda, shugaban na Najeriya ya ce, yana nazari kan korafin rashin sallamar manyan hafsoshin tsaronsa bayan tsanantar hare-haren Boko Haram a baya-bayan nan.

A wani lamar na daban, mun ji cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace bai chanja shugabannin tsaro bane domin guje ma “gasa a cikin ma’aikatar.”

Buhari ya bayyana hakan ne a hirar murya da aka nada daga gidan talbijin din Arise TV a daren ranar Litinin.

Shugaban ma’aikatan tsaro, Abayomi Gabriel Olonisakin, shugaban hafsan soji, Tukur Yusufu Buratai, shugaban hafsan sojin ruwa, Ibok-EteIkwe Ibas, da kuma shugaban hafsan sojin sama, Sadique Baba Abubakar, duk an tsawaita wa’adinsu sau biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel