Jirgin kasan Kaduna-Abuja ya samar da N960,000,000 ga gwamnatin Najeriya

Jirgin kasan Kaduna-Abuja ya samar da N960,000,000 ga gwamnatin Najeriya

Wuyan aiki ba’a fara ba, kamar yadda masu iya Magana kan ce, hakan yayi daidai da wani muhimmin aiki da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fara gadan gadan tun bayan darewarsa madafan iko, watau aikin farfado da sufurin jirgin kasa.

Zuwa yanzu dai za’a iya cewa kwalliya ta fara biyan sabulu, sakamakon wata sanarwa da hukula kula wa jiragen kasa na Najeriya, NRC, ta fitar a ranar Talata 8 ga watan Janairu, inda ta bayyana mamakon kudin shiga da ta samu a jiragen dake zuwa Kaduna zuwa Abuja kawai.

KU KARANTA: An kama mai kamawa: Gwamna Ambode ya cafke wani babban Soja yana cutar da jama’a

Majiyar Legit.com ta ruwaito shugaban hukumar, Fidet Okhiria ne ya bayyana haka, inda yace jirgin Kaduna zuwa Abuja ya samar da kimanin kudi naira miliyan tamanin(N80,000) a duk watan duniya a shekarar 2018.

Jirgin kasan Kaduna-Abuja ya samar da N960,000,000 ga gwamnatin Najeriya

Jirgin kasan Kaduna-Abuja
Source: Depositphotos

Mista Okhiria yace kididdiga sun nuna an fi samun kudi a shekarar 2018 fiye da shekarar 2017, inda yace ana samun naira miliyan goma sha shida, N16m, ne kacal a duk wata a shekarar 2017, amma fa duk da haka yace akwai sauran rina a kaba.

Domin kuwa Mista Okhiria yace har sai sun fara samun naira miliyan dari (N100,000,000) a wata ne hukumar zata fara samun riba, saboda har yanzu tana kashe akalla naira miliyan dari a wata wajen tafiyar da jiragen.

“Mun kusa kaiwa inda muke bukatan zuwa, saboda a lokacin da muka aiki muna samun naira miliyan goma sha shida ne a wata, amma muna kashe naira miliyan hamsin da shida, amma a yanzu kam mun samun naira miliyan tamanin, amma muna kashe miliyan 100.

“Don haka idan muka samu Karin taragon jirgi, da kuma Karin jiragen kansu, tabbas zamu kai ga nasara inda zamu fara samu riba, daga cikin matsalar da muke fama dashi a yanzu shine bamu da jirgin daukan kaya daga Kaduna zuwa Abuja, jirgin jigilar fasinja kadai muke da shi.

“Haka zalika matsalar wutar lantarki, domin kuwa a yanzu haka muna amfani da janareta ne wajen samar da wuta a duka tashoshinmu awa 24 a kowanne rana, wanda hakan ke ci mana litan gas dubu casa’in (99,000) a duk wata.” Inji shi.

Daga karshe shugaban NRC yace suna sa ran hada tashoshinsu da wutar lantarki a karshen watan Janairu, haka kuma yace a shekarar 2018 sun samu karin taragon jirgi guda hudu, akwai wasu sabbi guda goma dake tafe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel