Kurungus: PDP za ta garzaya Amurka, amma ban da Atiku

Kurungus: PDP za ta garzaya Amurka, amma ban da Atiku

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP za ta garzaya da yakin neman zabenta birnin Washington DC a mako mai zuwa amma dan takaran kujeran shugaban kasarta, Atiku Abubakar, ba zai samu damar zuwa ba.

Bisa ga rahoton, abokin tafiyan Atiku, Peter Obi, ne zai wakilcesa a taron da za'a gudanar a Amurka inda zai gabatar da manufofi, ayyuka, muradu da kuma ra'ayinsu kan hadaka tsakanin Amurka da Najeriya.

Jam'iyyar PDP zata hallara ne ranan Talata, 15 ga watan 2019 a cibiyar ilimin harkokin kasashen duniya wacce ta kware wajen bincike da taimakawa shugabannin duniya wajen basu shawari da kuma basu daman gabatar da muradunsu domin kawo cigaba a kasashensu.

Kurungus: PDP za ta garzaya Amurka, amma ban da Atiku

Kurungus: PDP za ta garzaya Amurka, amma ban da Atiku
Source: Depositphotos

Masu sharhi kan harkokin yau da kullum sun bayyana cewa rashin zuwan Atiku ya tabbatar da jita-jitan cewa yanada kashi a gindi kuma ba zai iya zuwa Amurka ba.

Kwanakin nan, kakakin kwamitin kamfen shugaba Buhari, Festus Keyamo, ya ce Alhaji Atiku Abubakar na da laifi a kasar Amurka kuma duk ranan da yaje, za'a gurfanar da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel