2019: zan samar da ayyuka rututu ga matasa, zan gyara Ajakuta – Alkawarin Atiku

2019: zan samar da ayyuka rututu ga matasa, zan gyara Ajakuta – Alkawarin Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, kuma dan takarar jam’iyyar PDP a matakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya dauki alkawarin samar da ayyuka rututu ga matasan Najeriya masu zaman banza, wannan shine muhimmin aikin da zai sa a gaba idan ya samu nasara.

Atiku ya bayyana haka ne a yayin ziyarar daya kai babban birnin jahar Kogi, Lakwaja, domin yakin neman zabensa, inda ya koka ka yadda adadin matasa marasa aikin yi ke cigaba da hauhawa, kamar yadda kididdigan alkalumma suka nuna.

KU KARANTA: An kama mai kamawa: Gwamna Ambode ya cafke wani babban Soja yana cutar da jama’a

A jawabinsa, Atiku ya bayyana manufar gwamnatinsa na tayar da komadar kamfanin sarrafa karafa na Najeriya dake garin Ajaokuta na jahar Kogi, wanda ya bayyana shi a matsayin kamfani daya tilo dake da damar samar ma miliyoyin matasa aiki.

Bugu da kari majiyar Legit.com ta ruwaito tsohon shugaban yana kokawa kan yadda talauci ke cigaba da mamaye yan Najeriya, wanda ya danganta musabbabin haka ga tabarbarewar tattalin arziki, don haka yace ya zama wajibi gwamnatinsa ta tayar da Ajaokuta, ko ba komai zata taimaka tattalin arzikin Najeriya.

A cigaba da jawabinsa da kuma alkawurran daya zayyana ma jama’an jahar Kogi, Atiku yace zai sauya fasalin kasar Najeriya, ta yadda al’ummar jahar Kogi zasu fi kowa cin mariyar albarkatun kasa dake makare a jahar.

“Ina cikin kunci a duk lokacin da na tuna halin talauci, rashi, da kuma kuncin rayuwa da yan Najeriya ke ciki, ga kuma matsalar rashin tabbataccen tsaro duka a Najeriya, duka wadannan matsaloli sun danganta ne ga rashin iya gudanar da mulki na jam’iyyar APC.

“Don haka ya zama wajibi akan jama’a daku zabi jam’iyyar PDP, tun daga sama har kasa domin mu taru mu canza wannan mummunan labara, ta haka ne zamu dawo da martabar Najeriya.” Inji Atiku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel