Ka da ka tsawaita wa'adin sufeto janar na 'yan sanda - Wani Lauyan Kano ya gargadi Buhari

Ka da ka tsawaita wa'adin sufeto janar na 'yan sanda - Wani Lauyan Kano ya gargadi Buhari

A yayin da ake ci gaba da barin baya da kura dangane da wa'adin sufeto janar na ‘yan sanda, Ibrahim Idris, wani fitaccen lauya na jihar Kano, Barrister Ali Jamilu, ya tsawatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a bisa tanadi na kudin tsarin mulkin kasa.

A yau Talata, gogaggen lauyan ya gargadi shugaban kasa Buhari akan tsawaita wa'adin babban sufeton na ‘yan sanda da ya yi bikin cikar sa shekaru sittin da haihuwa a ranar 3 ga watan Janairu.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, ana ci gaba da babatu dangane da tsawaita wa'adin babban jami'in na ‘yan sanda daga sassa daban-daban na kasar nan.

A cewar masanin dokar da kuma shari'a, ya ce ba bu wani tanadi cikin kundin tsari na dokokin kasar nan da sufeton ‘yan sanda Idris ya cancanci tsawaita wa'adin sa a bisa kujerarsa ta jagoranci.

Ka da ka tsawaita wa'adin sufeto janar na 'yan sanda - Wani Lauyan Kano ya gargadi Buhari

Ka da ka tsawaita wa'adin sufeto janar na 'yan sanda - Wani Lauyan Kano ya gargadi Buhari
Source: UGC

Tayar da jijiyar wuyan Lauyan ta biyo bayan rade-radin shiri da kuma yunkurin shugaba Buhari na tsawaita wa'adin sufeton na 'yan sanda yayin da babban zaben kasa ya gabato. Jamilu ya ce aiwatar da hakan na cin karo da kundin tsarin mulkin kasa.

Ko shakka ba bu kundin tsarin mulki na kasa ya yi tanadi na ajiye aiki ga duk wanda ya kai shekaru sittin a duniya ko kuma ya shafe tsawon shekaru talatin da biyar a karkashin aiki irin na gwamnatin Najeriya.

KARANTA KUMA: Jihar Kano da Legas na gaba ta fuskar yawan ma su zabe - INEC

Kazalika dokar kasa ta shar'anta ajiyar aiki ga duk wanda ya shafe shekaru talatin da biyar a karkashin aiki na gwamnati ko da kuwa shekarun sa na haihuwa ba su kai sittin ba.

Wannan lamari ya sanya zakakurin lauyan ke gargadin shugaba Buhari gami da taka masa birki da cewa kundin tsari mulki bai rataya masa wannan dama ba ta aiwatar da yadda yaso a yayin da ya so.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel