APC ta yi babban kamu a Ogun inda ta samu sabbin mambobi 2,000

APC ta yi babban kamu a Ogun inda ta samu sabbin mambobi 2,000

Rahotanni sun akwo cewa akalla mambobin jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP), Accord Party (AP) da Action Democratic Party (ADP) 2,000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Ogun.

Masu sauya shekar wadanda suka baro tsoffin jam’iyyunsu a ranar Litinin, 7 ga watan Janairu wajen kaddamar da kamfen din dan takarar gwamna a APC a jihar, Dapo Abiodun sun kuma kaddamar da goyon bayansu ga Abiodun.

An gudanar da taron ne a Atan, hedkwatar karamar hukumar Ijebu ta Arewa maso gabas da ke jihar.

APC ta yi babban kamu a Ogun inda ta samu sabbin mambobi 2,000

APC ta yi babban kamu a Ogun inda ta samu sabbin mambobi 2,000
Source: Depositphotos

Da yake jawabi ga mabiya jam’iyyar a wajen kamfen din, Abiodun yace gwamnatinsa za ta jajirce wajen cika dukkanin alkawaran zaben da ya dauka idan har yayi nasarar zama gwamna na gaba a jihar.

Ya kara da cewa gwamnatinsa na da burin cika dukkanin manufofin da ya rubuta sannan yayi alkawarin mayar da mulki ga shugabannin dukkanin kananan hukumomi a jihar.

KU KARANTA KUMA: Bana tsoron Sufeto Janar na yan sanda, zan dauki mataki – Buhari

A cewarsa zai yi hakan ne ta yadda ba zai shugabannin kananan hukumomin sun yi tattaki zuwa Abeokuta don rokon kudi daga gwamna ba kafin su iya aiwatar da lamuran hukumomin.

Ya kuma roki mazauna jihar da su fito su zabe shi kwansu da kwarkwatarsu domin hakan ne zai sa ya samu nasara a zaben gwamna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel