Maganar gaskiya: Ni ban umurci EFCC ta daina tuhumar Akpabio ba - Buhari

Maganar gaskiya: Ni ban umurci EFCC ta daina tuhumar Akpabio ba - Buhari

- Buhari ya karyata masu zargin cewa ya umurci hukumar EFCC da ta dakatar da tuhumar da take yiwa Sanata Godswill Akpabio, bayan da ya koma jam'iyyar APC

- Buhari ya bayyana wannan rahoto a matsayin kazafi, na cewar wai yana kare wasu jami'an gwamnati da ake zarginsu da cin hanci da rashawa

- Da aka tambaye shi ko hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na aiki akan ka'idoji da tsoron sa, ya ce, "Me ya sa zasu ji tsorona?"

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karyata masu zargin cewa ya umurci hukumar EFCC da ta dakatar da tuhumar da take yiwa Gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio, bayan da ya koma jam'iyyar APC a shekarar da ta koma.

Buhari ya bayyana hakan a lokacin tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise TV.

Shugaban kasar ya bayyana wannan rahoto a matsayin kazafi, na cewar wai yana kare wasu jami'an gwamnati da ake zarginsu da cin hanci da rashawa, yayinda su kuma a bangaren jam'iyyun hamayya ana tuhumarsu kullum.

KARANTA WANNAN: Matakin karshe: Babu karin albashi, babu zabe a 2019 - NLC

Gwamna Godswill Akpabio

Gwamna Godswill Akpabio
Source: Depositphotos

Da aka tambaye shi ko dalilin da ya sa Akpabio, wanda yake fuskantar tuhuma kan zargin karkatar da N100bn ba a ci gaba da tuhumar tasa ba tun bayan komawarsa APC, Buhari ya ce shima bai san dalili ba, kuma bai umurci EFCC ta dakatar da binciken ba.

Shugaban kasar ya ce: "Bana tunanin a lokacin da Akpabio ya dawo APC na umurci EFCC ta dakatar da tuhumar da take yi masa. Ba na jin zan iya tuna lokacin da na umurci EFCC, ko ICPC, rundunar 'yan sanda ko wata hukumar yaki da rashawa da ta saurarawa duk wani da ake zargi da cin hanci da rashawa.

"Ni ban aikata hakan ba, amma ina kalubalantar duk wadanda sukace nayi hakan, da su gabatar da hujja kan wannan zargi."

Da aka tambaye shi ko hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na aiki akan ka'idoji da tsoron sa, ya ce, "Me ya sa zasu ji tsorona?"

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel