CAF 2019: Za a buga gasar cin kofin Afrika a kasar Masar

CAF 2019: Za a buga gasar cin kofin Afrika a kasar Masar

Labari ya zo mana cewa an zabi kasar da za a doka gasar AFCON watau wasan cin kofin kwallon kafa na Nahiyar Afrika na 2019. A wannan shekarar za a sake fafatawa a gasar na kasashen Afrika.

CAF 2019: Za a buga gasar cin kofin Afrika a kasar Masar

A Misra za a buga gasar cin kofin Afrika na wannan shekarar
Source: Twitter

Kungiyar CAF mai kula da sha’anin kwallon kafa na Afrika ta zabi kasar Masar a matsayin inda za a doka gasar wassan kwallon kafa na shekarar nan. A yau Talata 8 ga Watan Disamba ne jami’an kungiyar CAF su ka dauki wannan mataki.

Kasar ta Masar ta samu damar daukar nauyin gasar na AFCON ne bayan zabe da aka yi dazu a Garin Dakar na kasar Senegal. Jami’an hukumar CAF ne su ka kada kuri’a inda Masar ta samu kuri’u mafi yawa a kan kasar Afrika ta kudu.

KU KARANTA: Alexis Sanchez zai kwashi makudan miliyoyi a Manchester United

An zabi kasar Larabawan ne bayan an karbe damar da aka ba kasar Kamaru na daukar nauyin gasar tun farko. Rashin isasshen shiri na filayen wasan kwallon kafan ya sa kungiyar CAF ta dauki matakin mikawa kasar Masar shirya gasar.

Sai dai kuma kungiyar kwallon kafan ta koka da halin siyasar da ake ciki a kasar Masar. A 2012 ne dai Mohammed Morsi ya kafa gwamnatin farar hula, sai dai an yi masa juyin mulki a tsakiyar 2013 inda Fateh Sisi ya dare mulki har i yau.

Jama’a za su zura idanu domin ganin yadda Masar za ta taka leda a gasar na shekarar nan. Masar tana ji da manyan ‘yan wasa wadanda su ka hada Mohammed Salah na kungiyar Liverpool.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel