Ambode ya kama direbobi dake tukin ganganci a Legas

Ambode ya kama direbobi dake tukin ganganci a Legas

Wasu direbobi da suka karya dokar tuki a kan titin Murtala Muhammed dake Ikeja a Legas sun gamu da fushin gwamna Ambode a yau, Litinin.

Ran gwamnan ya baci ne bisa ganin direbobi ke karya dokar tuki yayin da yake kan hanyar shiga garin Legas bayan dawowa daga taron kaddamar da kwamitin kamfen din Buhari da aka yi a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewar wani soja dake tuka wata mota mai lamba JJJ 290 AC ya fi bata wa gwamnan rai bisa yadda ya karya doka.

Ganin yadda sojan ke karya dokar tuki ne ya saka gwamna Ambode fitowa daga motar sa tare da kama sojan.

Wani direban dake tuka wata motar mai lamba LSR 445 ER ya gamu da fushin gwamnan bayan ya karya doka.

Nan take Ambode ya bayar da umarnin kama motocin tare da bayar da umarnin a gurfanar da direbobin bisa tuhumar su da karya dokokin tuki da gangan.

Ambode ya kama direbobi dake tukin ganganci a Legas

Ambode
Source: Depositphotos

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar Sanata maj wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya tofa albarkacin bakinsa a kan rahotannin dake yawo na zargin Sanata Dino Melaye da yiwa Buhari ihu lokacin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a gaban mambobin majalisar.

A ranar 19 ga watan Disamba ne wasu daga cikin mambobin majalisar tarayya suka yiwa Buhari ihu a lokacin da yake gabatar da jawabi a kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu yayin gabatar da kunshin kasafin kudin shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Zan kawo karshen ware kunshin kudin tsaro a Kano - Abba K. Yusif

Sanata Dino Melaye, mai wakiltar mazabar jihar Kogi ta yamma, ya musanta cewar yana daga cikin mambobin majalisar da suka yiwa Buhari ihu.

Tun bayan faruwar hakan, rahotanni a dandalin sada zumunta ke nuna cewar Melaye ne ya jagoranci yiwa Buhari ihu a zauren majalisar.

Da yake kare kansa, Melaye ya ce bai yiwa Buhari ihu ba tare da bayyana cewar bai ma halarci zaman majalisa na ranar ba.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a kan wannan zargi da ake yiwa Melaye a shafinsa na Tuwita, Shehu Sani ya gaskata Sanata Melaye a kan cewar ba ya zauren majalisa a ranar da aka yiwa Buhari ihu.

"Sanata Dino Melaye bai halarci zaman majalisa ba a ranar da aka yiwa Buhari ihu," kamar yadda Shehu Sani ya rubuta a shafinsa na Tuwita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel