An kama mai kamawa: Gwamna Ambode ya cafke wani babban Soja yana cutar da jama’a (Hoto)

An kama mai kamawa: Gwamna Ambode ya cafke wani babban Soja yana cutar da jama’a (Hoto)

Kamar yadda malam bahaushe ke cewa an kama mai kamawa, ko kuma wai mai dokar barci ya bige da gyangyadi, ma’ana hakan na faruwa idan har ta kansance wanda aka baiwa hakki yaci amana, kamar yadda ta kasance da wani Soja a Legas.

Gwamnan jahar Legas Akinwumi Ambode ya samu nasarar cafke wani jami’in Soja yayin da yake tukin ganganci tare da yi ma dokar tuki karan tsaye akan titin filin sauka da tashin jirage na Murtala Muhammed.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna Ilaihi rajiun: Gobara ta halaka kananan yara 2 a Kano

An kama mai kamawa: Gwamna Ambode ya cafke wani babban Soja yana cutar da jama’a (Hoto)

Ambode
Source: Original

Kaakakin gwamnan, Habib Haruna ne ya bayyana yadda lamarin ya kasance cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata 8 ga watan Janairu a garin Ikeja na jahar Legas, inda yace Gwamna Ambode ya damu matuka da yadda jama’an Legas suke kin mutunta dokokin hanya da gangan.

A ranar Litinin 7 ga watan Janairu yayin da gwamnan ke kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya dawo daga babban birnin tarayya Abuja inda ya halarci wasu uzurorinsa ne ya kama wani hafsan Soja yana tuka wata mota kirar Space Bus mai lamba JJJ 290 AC ya ari hanyar masu tafiya shi kadai saboda gadara.

An kama mai kamawa: Gwamna Ambode ya cafke wani babban Soja yana cutar da jama’a (Hoto)

Ambode
Source: Original

Hangen Sojan keda wuya, gwamnan yayi zumbur ya fito daga cikin motarsa, inda ya tare motar Sojan, tare da ja masa kunne da kuma nuna bacin ransa da yadda yake karya dokar hanya, ba kamar yadda aka san Sojoji da bin doka da oda ba.

Wannan laifi da Sojan ya aikata yasa gwamnan jahar Legas ya bada umarnin a kwace motar tasa, kuma a mika ta ga hukumar kulawa dokokin tuki ta jahar Legas, sa’annan ya umarci hukumar ta tabbata ta shigar da karar Sojan da duk wanda aka kama yana karyar dokar hanya gaban kotu don yanke masa hukuncin daya dace dashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel