Bana tsoron Sufeto Janar na yan sanda, zan dauki mataki – Buhari

Bana tsoron Sufeto Janar na yan sanda, zan dauki mataki – Buhari

- Shugaban Kasa Buhari yace bai chanja shugabannin tsaro bane domin guje ma gasa a cikin ma’aikatar

- Shugaban rundunar yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris wanda ake sanya ran zai yi ritaya a ranar 3 ga watan Janairu bayan ya kammala shekaru 35 akan aiki na ci gaba da gudanar da aikinsa

- Buhari yace zai dauki mataki cewa shi baya tsron sufeto janar na yan sandan

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace bai chanja shugabannin tsaro bane domin guje ma “gasa a cikin ma’aikatar.”

Buhari ya bayyana hakan ne a hirar murya da aka nada daga gidan talbijin din Arise TV a daren ranar Litinin.

Shugaban ma’aikatan tsaro ,Abayomi Gabriel Olonisakin, shugaban hafsan soji, Tukur Yusufu Buratai, shugaban hafsan sojin ruwa, Ibok-EteIkwe Ibas, da kuma shugaban hafsan sojin sama, Sadique Baba Abubakar, duk an tsawaita wa’adinsu sau biyu.

Bana tsoron Sufeto Janar na yan sanda zan dauki mataki – Buhari

Bana tsoron Sufeto Janar na yan sanda zan dauki mataki – Buhari
Source: Depositphotos

Hakazalika, shugaban rundunar yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris wanda ake sanya ran zai yi ritaya a ranar 3 ga watan Janairu bayan ya kammala shekaru 35 akan aiki na ci gaba da gudanar da aikinsa.

Shugaban kasar yace; “ya zama dole shugaba yayi taka-tsan-tsan sosai domin baka san kudirin wadanda ke tasowa ba.”

KU KARANTA KUMA: 2019: Buhari na yaudarar Tinubu ne kawai - Afenifere

Yace kokarin shugabannin tsaron na iya zama ba yadda aka yi zato ba amma shi zai dauki alhakin hakan kan rashin chanja su da baiyi ba.

Da aka tambaye shi musamman game da IGP, shugaban kasar yace; “bana tunanin ina tsoronsa. Zan dauki mataki.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel