Karancin albashi: Ma’aikatan Najeriya zasu kaurace ma zaben 2019 gaba daya – NLC

Karancin albashi: Ma’aikatan Najeriya zasu kaurace ma zaben 2019 gaba daya – NLC

Hadaddiyar kungiyar kwadago dake wakiltar kafatanin ma’aikatan Najeriya ta bayyana cewa zata kaurace ma zaben 2019 gaba daya, matukar gwamnatin tarayya bata mika ma majalisa kudurin dokar Karin karancin albashi zuwa N30,000 ba.

Da wannan sanarwa, NLC na nufin babu ma’aikacin da zai kada kuri’a a yayin zabukan shekarar 2019 kenan, kamar yadda shugaban NLC reshen jahar Edo, Emmanuel Ademokun ya bayyana a ranar Talata 8 ga watan Janairu a garin Bini.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna Ilaihi rajiun: Gobara ta halaka kananan yara 2 a Kano

Shugaba Aemokun ya bayyana haka ne yayin da ma’aikata suka yi ma fadar gwamnatin jahar Edo tsinke a yayin da suke gudanar da zanga zangar nuna bacin ransu da cigaba da rikon sakainar kashi da gwamnati keyi ma batun Karin karancin albashin.

Legit.com ta ruwaito shi yana cewa “Ma’aikatan Najeriya ne suke karbar albashi mafi karanci a duniya gaba daya, don kodai a tabbatar da karancin albashi zuwa N30,000 gabanin lokacin zaben 2019, ko kuma mu kaurace ma zaben gaba daya.

“Mun zo nan ne domin mu bayyana bacin ranmu game da kin aika ma majalisun dokokin Najeriya kudurin dokar sabon karancin albashi da gwamnatin tarayya ta gaza yi, saboda muna da labarin tuni aka mika ma Buhari kudurin, don haka dole ne ma’aikata su tantance wadanda zasu shugabancesu.” Inji shi.

Sai dai daga karshe shugaban NLC na jahar Edo yace kungiyarsu bata da wata matsala da gwamnatin jahar Edo a karkashin jagorancin Gwamna Godwin Obaseki, musamman yadda take biyan ma’aikata hakkokinsu, kuma tayi alkawarin biyan sabon karancin albashi N30,000 da zarar ya zama doka.

A nasa jawabin, gwamnan jahar, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jahar, Isaac Ehiozuwa ya yaba da yadda kungiyar ta gudanar da zanga zangarta cikin lumana, inda yace jahar Edo ce kan gaba wajen kula da walwalar ma’aikata, a cewarsa N25,000 suke biya a matsayin karancin albashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel