Na bar APC ne saboda Buhari ya ki amsa kira na - Na hannun damar shugaban kasa

Na bar APC ne saboda Buhari ya ki amsa kira na - Na hannun damar shugaban kasa

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin tsohuwar jam'iyyar CPC a shekarar 2011, Alhaji Haruna Saeed, dake da kusanci da shugaba Buhari ya fita daga jam'iyyar APC ne saboda Buhari ya ki amsa kiransa ko sakannin da ya yi masa bayan ya lashe zaben shekarar 2015.

Fusataccen dan siyasar ya shaidawa magoya bayansa a karshen makon jiya cewar shugaba Buhari ya yi watsi da duk wadanda suka yi masa wahala lokacin yakin neman zabensa a shekarar 2015.

Da yake magana a kan takarar gwamnan da ya yi a 2011, Saeed ya ce, "na yi takara da marigayi Ibrahim Yakowa, kuma nine ke kan gaba kafin jami'an hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) su dakatar da sanar da sakamako sannan daga bisani jami'an tsaro suka sa dokar hana fita, washe gari kuma aka sanar da cewar Yakowa ya lashe zaben."

Saeed, tsohon babban akawun jihar Kaduna a mulki soji karkashin Birgediya janar Jafaru Isa da mulkin farar hula karkashin Ahmad Makarfi, ya ce hatta kotun sauraron karar zabe ta bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara amma daga baya kotun daukaka kara ta soke hukuncin.

Na bar APC ne saboda Buhari ya ki amsa kira na - Na hannun damar shugaban kasa

Na bar APC ne saboda Buhari ya ki amsa kira na - Na hannun damar shugaban kasa
Source: Depositphotos

A cewar sa, Buhari ne a lokacin ya kira shi ya bashi shawarar cewa kar ya bata kudinsa a shari'a domin ba za ai masa adalci ba.

Kazalika ya shaidawa magoya bayan nasa cewar bayan shugaba Buhari ya ki amsa kira da sakonninsa, ya kama kafa da Jafaru Isa da Tinubu domin ya gana da Buhari ko kwangila ake bashi a gwamnati amma duk da haka bai samu ganin Buhari ba.

DUBA WANNAN: Boko Haram: Kashim Shettima ya jagoranci dattijan jihar Borno zuwa wurin Buhari, hotuna

Saeed ya kara da cewa a wannan gaba, bashi da wani zabi da ya wuce ya fita daga APC saboda wasu 'yan tsirarun mutane sun saka jam'iyyar a aljihu a matakin tarayya da na jiha.

Sai dai duk da ya bayyana ficewar sa daga APC, Saeed bai ambaci dan takarar shugaban kasa da yake so magoya bayansa su zaba ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel