Matakin karshe: Babu karin albashi, babu zabe a 2019 - NLC

Matakin karshe: Babu karin albashi, babu zabe a 2019 - NLC

- Kungiyar kwadago NLC ta ce ba zata shiga cikin zaben 2019 ba, ma damar gwamnatin tarayya ta gaza kaddamar da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi

- NLC ta zargi gwamnatin shugaban kasa Buhari da yin wasa da hankalin ma'aikatan kasar ta hanyar daukar alkawurra da dama ba tare da cikawa ba

- Kungiyar ta bukaci Buhari da ya gaggauta mikawa majalisar dokokin kasar dokar sabunta albashi mafi karancin, tare da kaddamar da shi ba tare bata lokaci ba

Kungiyar kwadago NLC reshen jihar Cross River, ta ce ba zata shiga cikin zaben 2019 ba, ma damar gwamnatin tarayya ta gaza kaddamar da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar.

Shugaban kungiyar NLC na jihar, Mr John Ushie, ya bayyana hakan a ranar Talata a yayin da mambobin kungiyar suka gudanar da zanga zangar lumana don ganin cewa gwamnatin tarayyar ta kaddamar da wannan albashi mafi karanci.

Ushie ya ce albashi mafi karanci na ma'aikatan a yanzu, N18,000 ya kamata ya canja tun 2015, kuma ya zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da yin wasa da hankalin ma'aikatan kasar ta hanyar daukar alkawurra da dama ba tare da cikawa ba.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: Hausa/Fulani a jihar Oyo sun sha alwashin kadawa Buhari kuri'u 700,000

Matakin karshe: Babu karin albashi, babu zabe a 2019 - NLC

Matakin karshe: Babu karin albashi, babu zabe a 2019 - NLC
Source: Twitter

Shugaban kungiyar ya koka kan dogon lokacin da dokar sabunta albashi mafi karancin a gaban shugaban kasa Buhari ba tare da wani tsari na gabatar da shi gaban majalisundokokin kasar don zama doka ba.

"Kungiyar kwadago zata ci gaba da fafutuka har sai ta samu nasara. Nasara bata zuwa cikin sauki, tana bukatar dagewa da aiki tukuru, kuma tana bukatar kowa ya bayar da gudunmowarsa. Ya kamata ace tun 2015 tsohon albashi mafi karancin ya canja. Hakurin ma'aikata ya kare, don haka mune zamu yanke hukuncin makomarmu da kanmu.

"Haka zalika, muna aikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta mikawa majalisar dokokin kasar dokar sabunta albashi mafi karancin, tare da kaddamar da shi ba tare bata lokaci ba.

"Idan kuwa gwamnatin tarayya ta gaza kaddamar da albashi mafi karanci ga ma'aikata, to kuwa babu dalilin da zaisa mu shiga cikin zaben 2019, wannan shine matakin da muka dauka na karshe," a cewar shugaba kungiyar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel