Mazauna kauyen Pakudi sun tsere daga muhallansu bayan wani manomi ya kashe makiyayi

Mazauna kauyen Pakudi sun tsere daga muhallansu bayan wani manomi ya kashe makiyayi

Mazauna garin Pakudi da ke karamar hukumar Obafemi-Owode na jihar Ogun sun gudu daga muhallansu bayan wani manomi a garin ya kashe makiyayi sakamakon rashin jituwa da suka samu kan gonar manomin.

Manema labarai sun tattaro cewa tun lokacin da wannan abu ya faru a ranan Laraban da ya gabata, mazauna garin sun tattara inasu-inasu domin tsoron ramuwar gayya daga Makiyaya.

A daidai lokacin da jaridar Punch ta kai ziyara garin, kusan dukkan mutanen garin guje daga muhallansu.

Kauyen Pakudi wata kauyece dake kusa da babban birnin jihar Ogun, Abeokuta.

Bincike ya nuna cewa jami'an yan sanda sun dira garin bayan wannan faruwan kuma suka damke wasu da ake zargi da kisan amma an sakesu daga bayan bincike. Amma an damke uwargidar manomin a yanzu.

Rahoto ya nuna cewa manomin ya kashe Fulani makiyayin a cikin gonarsa kuma ya dauke dukiyarsa.

Wani majiya da muka sakaye sunansa ya bayyana cewa manomin dan asalin jihar Benuwe ne amma ya zo cin damina a kauyen.

Yace: "Wannan ne karo na farko da zamuji irin wannan abun. Kauyen nan ta kasance cikin zaman lafiya kafin wannan faruwan."

"Zuwa yanzu, yawancin mazauna kauyen sun gudu domin tsoron rayukansu saboda sun samu labarin cewa Fulani makiyaya suna shirin kawo harin ramuwar gayya kauyen."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel