Butulu: Najeriya ta yi asarar $2.8bn a 2018 sakamakon badakalan man fetur - Majalisar dinkin duniya

Butulu: Najeriya ta yi asarar $2.8bn a 2018 sakamakon badakalan man fetur - Majalisar dinkin duniya

Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa kasar Najeriya ta yi asarar kimanin kudi dala biyan uku, musamman sakamakon badakalan arzikin man fetur.

Wata rahoton da sakataren majalisar dinkin duniya, Antoni Gutteres ya saki kan harkokin majalisar a yankin Afrika maso yamma ranan Litinin, 7 ga watan Junairu a birnin New York.

Rahoton wacce ta yi bayanin lissafi da akayi daga watan Yulin 2018 zuwa karshen shekara, an bayyana cewa satan man fetur babban kalubale ne ga zaman lafiya, tsaro, da cigaban yankin.

"Laifuffukan man fetur ya sabbaba asaran kimanin 2.8 billion dollars na kudin shiga a bara a Najeriya."

"Tsakanin watan Junairu zuwa Nuwamba, an samu rahotannin satan mai 82 a yankin Guinea."

KU KARANTA: Sarkin Malaysia yayi murabus don ya auri sarauniyar kyan Rasha

A bangare guda, Jim Yong Kim, babban bankin duniya, yayi murabus a jiya litinin, bagatatan bayan wa'adin aikinsa sai a 2022 ne zai kare.

A takardar da ya rattabawa hannu, yace daga watan gobe, ya gama aikinsa na bankin duniya, sai dai a nemo wani a bashi, shi kam baya yi.

Albashin kujerar tasa dai, yafi naira biliyan daya in aka juya daga dala, amma tahalikin yace baya so ya gaji, a kai kasuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel