Zaben 2019: Hausa/Fulani a jihar Oyo sun sha alwashin kadawa Buhari kuri'u 700,000

Zaben 2019: Hausa/Fulani a jihar Oyo sun sha alwashin kadawa Buhari kuri'u 700,000

- Hausawa da Fulani da ke zaune a jihar Oyo sun lashi takobin kadawa Buhari kuri'u 700,000 a zabe mai zuwa, don bashi damar zarcewa akan mulkin kasar

- Kungiyar FULBE, ta kaddamar da kodinetoci a kanana hukumomi 33 na jihar da nufin zakulo 'yayan kungiyar da zasu yiwa Buhari yakin zabe

- Sama da mambobi 10,000 na kungiyar FULBE ne suka halarci taron inda gwamnan jihar, Abiola Ajimobi, ya samu wakilcin kwamishinan ayyuka da zirga-zirga, Wasiu Dauda

Hausawa da Fulani da ke zaune a fadin gundumomi 315 da ke cikin kananan hukumomi 33 na jihar Oyo sun lashi takobin kadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri'u 700,000 a ranar 16 ga watan Fabreru, don bashi damar zarcewa akan mulkin kasar.

Sunyi wannan alkawarin ne a lokacin kaddamar da kungiyar yakin zaben Buhari/Osinbajo karkashin Fulani, Hausa, da aka fi sani da FULBE a jiahr Oyo, a garin Iseyin da ke jihar.

Jami'ar hulda da jama'a na kungiyar FULBE reshen jihar, Amina Abdullahi, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi ta ruwaito kodinetan kundiyar FULBE na kasa, Alhaji Mohammed Dan Alli, yana cewa babu ja da baya a kan wannan kudiri nasu na yin gangami don marabawa shugaban kasa Buhari da Yemis Osinbajo baya a zaben watan Fabreru.

KARANTA WANNAN: Asiri ya tonu: Yadda aka shirya kashe Atiku, Saraki a wajen yakin zabe

Zaben 2019: Hausa/Fulani a jihar Oyo sun sha alwashin kadawa Buhari kuri'u 700,000

Zaben 2019: Hausa/Fulani a jihar Oyo sun sha alwashin kadawa Buhari kuri'u 700,000
Source: Facebook

Tace domin cimma wannan kudurin, sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Aminu Suleiman, ya kaddamar da kodinetoci a kanana hukumomi 33 na jihar da kuma babban kodineta na jiha da nufin shiga lungu da sako don zakulo 'yayan kungiyar da zasu yiwa Buhari yakin zabe.

Sanarwar ta kara da ruwaito kodinetan jihar, Alhaji Abdullahi Umar, yana cewa, zasu baiwa Buhari kuri'un gaba daya 'yayan kungiyar tasu da suka kai kimanin 700,000, wadanda sun isa kada kuri'a kuma sun mallaki katunan zabensu.

Sama da mambobi 10,000 na kungiyar FULBE ne suka samu damar halartar taron inda gwamnan jihar, Abiola Ajimobi, ya samu wakilcin kwamishinan ayyuka da zirga-zirga, Wasiu Dauda.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel