Matakin farko da ya kamata gwamnati ta dauka na yaki da cin hanci da rashawa shine tabbatar da yiwa talakawa aiki - Atiku

Matakin farko da ya kamata gwamnati ta dauka na yaki da cin hanci da rashawa shine tabbatar da yiwa talakawa aiki - Atiku

- Dan takarar jam’iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yace matakin farko da ya kamata gwamnati ta dauka na yaki da cin hanci da rashawa shine tabbatar da yiwa talakawa aiki da samar masu da hanyoyin dogaro da kai

- Atiku yace wajibi ne ‘yan kasa su sami wadata ta kowacce hanya, in sana’a suke yi, ko aikin gwamnati suke yi da sauransu

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar yace matakin farko da ya kamata gwamnati ta dauka na yaki da cin hanci da rashawa shine tabbatar da yiwa talakawa aiki da samar masu da hanyoyin dogaro da kai da biyan bukatunsu na yau da kullum.

A cewar Atiku wajibi ne ‘yan kasa su sami wadata ta kowacce hanya, in sana’a suke yi, in aikin gwamnati suke yi da sauransu.

Matakin farko da ya kamata gwamnati ta dauka na yaki da cin hanci da rashawa shine tabbatar da yiwa talakawa aiki - Atiku

Matakin farko da ya kamata gwamnati ta dauka na yaki da cin hanci da rashawa shine tabbatar da yiwa talakawa aiki - Atiku
Source: Depositphotos

Da aka tambaye shi ko yana ganin rashin kiyaye doka da oda ne yasa aka gaza shawo kan matsalar cin hanci da rashawa, sai Atiku yace baya ganin haka, kasancewa ana kama wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa ana tuhumarsu, ana kuma hukunta wadanda aka samu da laifi.

KU KARANTA KUMA: Karancin albashi: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago za su sake zama a yau da karfe 1

Dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa, irin rawar da ya taka a samar da ayyukan yi, da kwarewa da yake da ita wajen kirkiro da masana’atu zai taimaka mashi wajen shawo kan matsalar rashin aikin yi musamman tsakanin matasa.

Dangane da batun sauya sheka, yace shi da dan takarar jam’iyar APC, shugaba Muhammadu Buhari dukansu sun canza sheka sau da dama, wanda ‘yanci ne da kowanne dan kasa yake da shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel