Karancin albashi: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago za su sake zama a yau da karfe 1

Karancin albashi: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago za su sake zama a yau da karfe 1

- Gwamnatin tarayya tace za ta sake zama da kungiyar kwadago na kasa domin hana barazanar kungiyar akan rashin mika dokar karin mafi karancin albashi ga majalisar dokokin kasar da karfe 1pm na ranar Talata

- Kwamitin masu ruwa da tsaki na NLC sun yi barazanar yin zanga-zangar gama gari a ranar 8 ga watan Janairu, idan har gwamnatin tarayya ta ki mika dokar karin albashi ga majalisar dokokin kasar

- Shugaban NLC ya bayyana cewa kungiyar kwadagon ta yi zantawa mai amfani tare da gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya tace za ta sake zama da kungiyar kwadago na kasa domin hana barazanar kungiyar akan rashin mika dokar karin mafi karancin albashi ga majalisar dokokin kasar da karfe 1pm na ranar Talata, 8 ga watan Janairu.

Sanata Chris Ngige, ministan kwadago da daukar aiki ya bayyana hakana yayinda yake zantawa da manema labarai bayan wani ganawar sirri da kungiyar kwadagon a ranar Talata a Abuja.

Karancin albashi: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago za su sake zama a yau da karfe 1

Karancin albashi: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago za su sake zama a yau da karfe 1
Source: Depositphotos

Ku tuna cewa kwamitin masu ruwa da tsaki na NLC sun yi barazanar yin zanga-zangar gama gari a ranar 8 ga watan Janairu, idan har gwamnatin tarayya ta ki mika dokar karin albashi ga majalisar dokokin kasar.

Kungiyar kwadagon ta yi barazanar ne biyo bayan jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kafa wata kwamitin da za su duba hanyoyin tabbatar da cewa karin albashin bai kai ga tashin yawan ciwo bashi ba.

A cewar Ngige, “mun yi kokari kuma a ranar Talata, za mu san ainahin ranar da za a mika dokar ga majalisar dokoki.

“Akwai matukar wuya tsayar da rana domin akwai tsare-tsaren da za a bi kan dokar."

KU KARANTA KUMA: Bai kamata a sake zabar gwamnonin da basu yi aiki ba - Buhari

Da yake Magana a nashi bangaren, Mista Ayuba Waba, shugaban NLC ya bayyana cewa kungiyar kwadagon ta yi zantawa mai amfani tare da gwamnatin tarayya.

Ya bayyana cewa shugabannin kungiyar kwadagon sun zanta sannan sun amince da sake zama da gwamnatin Tarayya a ranar Talata da karfe 1pm domin tabbatar da cewa ba a sake samun jinkiri ba wajen gabatar da dokar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel