Gwamna Masari: Katsina zata dauki matakan da suka dace na kawo karshen ta'addanci

Gwamna Masari: Katsina zata dauki matakan da suka dace na kawo karshen ta'addanci

- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce zai dauki dukkanin matakan da ya dace na kawo karshen matsalolin tsaro da ke fuskatar jihar

- Masari , ya kuma yi nuni da cewa gwamnatin jihar zata ci gaba da hadin guiwa da jami'an tsaro don cimma wannan kudiri

- Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa tuni ta kulla yarjejeniya da hukumomin jamhuriyyar Niger don dakile matsalolin tsaro akan iyakokin kasar

Gwamnatin jihar Katsina ta ce zata dauki dukkanin matakan da ya dace na kawo karshen matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

Gwamnan jihar, Aminu Masari, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin a Kankara, a lokacin da yake kaddamar da yakin zabensa a karo na biyu, ya kuma yi nuni da cewa gwamnatin jihar zata ci gaba da hadin guiwa da jami'an tsaro don cimma wannan kudiri.

Ya ce: "Gwamna na a shirye don samar da wasu matakai da zasu bunkasa sha'anin tsaro da kuma ayyukan jami'an tsaro na jihar. Babu wata gwamnati mai adalci da zata yarda da fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma satar shanu, ba tare da ta dauki matakai na dakile wadannan ta'addancin ba."

KARANTA WANNAN: Anzo wajen: Dino Melaye ya samu lafiya, zai iya fuskantar shari'a yanzu - Asibitin 'yan sanda

Gwamna Masari: Katsina zata dauki matakan da suka dace na kawo karshen ta'addanci

Gwamna Masari: Katsina zata dauki matakan da suka dace na kawo karshen ta'addanci
Source: UGC

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa tuni ta kulla yarjejeniya da hukumomin jamhuriyyar Niger don dakile matsalolin tsaro akan iyakokin kasar.

Masari ya ce Nigeria da jami'an tsaronta zasu yi hadaka wajen kawo karshen ta'addancin da ke addabar kasar.

Ya yi kira ga daukacin al'ummar jihar da su ci gaa da baiwa jami'an tsaro muhimman bayanai da suka shafi ta'addanci da 'yan ta'adda.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel