Bai kamata a sake zabar gwamnonin da basu yi aiki ba - Buhari

Bai kamata a sake zabar gwamnonin da basu yi aiki ba - Buhari

Shugaban kasa kuma dan takarar shugabancin kasa a karkashin APC a zabe mai zuwa, Muhammadu Buhari ya ce bai kamata talakawa su sake zabar gwamnonin da basu yi masu aiki ba, da ya hada da gaza biyan albashin ma’aikata.

Shugaban kasarya bayyana cewa, ya kamata masu kada kuri’a su zabi ‘yan takara bisa cancanta da kuma aikin da suka yiwa talakawa, ba wai la’akari da wani abu na daban ba.

A hirarshi da muryar Amurka, Buhari yace bai ga dalilin da zai sa gwamnatin tarayya ta ba gwamnoni kudi domin gudanar da ayyuka amma su gaza biyan albashi ba. Yace yana mamakin yadda gwamnoni zasu iya zuwa su kwanta su yi barci bayan sun san akwai mutanen dake aikin gwamnatin basu biya su albashinsu ba, sanin suna da gidaje, suna da iyali, basu biya kudin haya ba, basu biya bukatun iyalansu ba, da suka hada da biyan kudin makaranta, da zuwa asibiti da sayen abinci.

Bai kamata a sake zabar gwamnonin da basu yi aiki ba - Buhari

Bai kamata a sake zabar gwamnonin da basu yi aiki ba - Buhari
Source: Depositphotos

Shugaba Buhari yace tsarin dokar kasar ya ba gwamnonin ‘yancin kashe kudin da suka samu ba tare da tsangwama ba, sai dai wannan ya zama damar da wadansu suke fakewa suna kin yiwa al’umma aiki. Sabili da haka ya shawarci talakawa su yi amfani da ‘yancinsu na zabe su zabi wadanda suka san zasu yi masu aiki.

KU KARANTA KUMA: Kudirin shugabancin Atiku ya hadu da cikas yayinda Buhari ya tarbi yan PDP daga arewa maso gabas

Dangane da batun yaki da cin hanci da rashawa, shugaba Buhari yace hanyar da yake bi a halin yanzu ita ce hanyar da tsarin damokaradiya ya yarda da shi. Yace a baya ya dauki wani mataki na dabam, amma kasancewa yanzu ana mulkin damokaradiya ne tilas yabi tsarin. Sai dai yace duk da yake tsarin yana daukar lokaci, duk da haka, haka na cimma ruwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel