Na yi alkawarin habaka nagartar dakarun tsaro - Buhari

Na yi alkawarin habaka nagartar dakarun tsaro - Buhari

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima da kuma tawagar dattawan jihar sa, a jiya Litinin sun yi dandazo wajen ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin fadarsa ta Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Ganawar ta gudana ne biyo bayan sake kunno kai da kuma ta'zzarar tayar da kayar baya ta kungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya musamman jihar Borno da a halin yanzu rayuka da dama sun salwanta.

Gwamna Shettima, cikin zubar hawaye ya shigar da koken sa ga shugaban kasa Buhari kan kara kaimi da mikewarsa tsaye gami da fafutika ta yakar ta'addancin Boko Haram da ta kasance daya daga cikin dalilai da ya sanya al'ummar kasa su ka kada ma sa kuri'u a zaben 2015.

Shugaba Buhari da sanadin karfin iko na kujerarsa ta mulki, ya sha alwashin tabbatar da inganci gami da habaka nagarta ta dukkanin dakarun tsaro domin cin galaba kan 'yan ta'adda a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Na yi alkawarin habaka nagartar dakarun tsaro - Buhari

Na yi alkawarin habaka nagartar dakarun tsaro - Buhari
Source: Twitter

Jagoran na kasa ya sha alwashin tanadar ingatattun makamai ga dakarun sojin kasar nan tare da inganta jin dadin su ta kowace fuska domin ci gaba da tunkarar ta'addancin dukkanin masu ta'ada a fadin Najeriya baki daya.

Buhari ya kuma shaidawa gwamnan cewa, tabbatar da tsare rayuka da kuma bayar da kariya ga dukiyoyin al'umma za ta ci gaba da kasancewa babban jigo mai muhimmancin gaske a karkashin gwamnatin sa.

KARANTA KUMA: Ba bu dalibin mu da aka kashe ko aka yi garkuwa da shi - Jami'ar Al-Qalam

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tawagar gwamna Kashim ta hadar da jiga-jigan 'yan siyasa, Sarakunan gargajiya, jagororin addini, Mata da kuma shugabannin kafofin watsa labarai na jihar sa.

Daga bangaren gwamnatin tarayya kuma mahalarta taron sun hadar da; shugaban hafsin dakarun soji, babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa, shugaban hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS da shugaban hukumar leken asiri ta NIA.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel