Anzo wajen: Dino Melaye ya samu lafiya, zai iya fuskantar shari'a yanzu - Asibitin 'yan sanda

Anzo wajen: Dino Melaye ya samu lafiya, zai iya fuskantar shari'a yanzu - Asibitin 'yan sanda

- Asibitin rundunar 'yan sanda dake Garki, Abuja, ya tabbatar da cewa a yanzu sanata Dino Melaye, ya samu cikakkar lafiyar da za a gurfanar da shi gaban kotu

- Sai dai, Melaye ya bukaci rundunar 'yan sanda da ta dauke shi daga wannan asibitin tare da mayar da shi wani babban asibiti na kasa

Rundunar 'yan sandan ta bayyana wannan bukata ta sanatan a matsayin wani wasan kwaikwayo, inda IG Amadu ya kalubalanci bayanin lafiyar Melaye da ya gabatar

Asibitin rundunar 'yan sanda dake Garki, Abuja, ya tabbatar da cewa a yanzu sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya samu cikakkar lafiyar da za a gurfanar da shi gaban kotu, don fuskantar tuhumar zargin da ake yi masa, na yunkurin kisan kai.

Bayanin hakan ya biyo bayan gwa gwaje da asibitin ya gudanar akan sanata, wanda suka tabbatar da cewa yana da cikakkar lafiyar da zai iya gurfana gaban kotu.

Mataimakin Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda (AIG) da ke kula da asibitin Kaomi Amadu, ya ce an yanke wannan hukunci ne bayan da sanatan ya yi ikirarin cewa bashi da isassar lafiyar da zai iya fuskantar tuhumar da ake masa, wanda a cewar mataimakin Sifetan, gwaje gwajen sun karyata wannan ikirari na Melaye.

KARANTA WANNAN: Boko Haram: Jihar Borno ta gabatarwa Buhari manyan bukatu 10

Anzo wajen: Dino Melaye ya samu lafiya, zai iya fuskantar tuhuma yanzu - Asibitin 'yan sanda

Anzo wajen: Dino Melaye ya samu lafiya, zai iya fuskantar tuhuma yanzu - Asibitin 'yan sanda
Source: Facebook

Sai dai, Melaye ya bukaci rundunar 'yan sanda da ta dauke shi daga wannan asibitin tare da mayar da shi wani babban asibiti na kasa, bayan kwanaki uku da samun kulawa a hannun likitocin asibitin rundunar.

Rundunar 'yan sandan ta bayyana wannan bukata ta sanatan a matsayin wani wasan kwaikwayo, inda IG Amadu ya kalubalanci bayanin lafiyar Melaye da ya gabatar.

Melaye, wanda ya buya a gidansa na tsawon kwanaki 8, daga karshe ya mika wuyansa ga rundunar 'yan sanda a karshen makon da ya gabata, bayan wata 'yar tataburza, daga karshe ya zub e kasa sumamme, wanda aka garzaya da shi asibiti.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana Dino Melaye a matsayin wanda take nema ruwa a jalo sakamakkon zarginsa da yunkurin kisan kai a ranar 19 ga watan Yulin 2018, inda shi da 'yan bangar siyasarsa suka harbi wani jami'in rundunar yan sanda, Sajen Danjuma Saliu, a bakin aikinsa, a kan titin Aiyetoro Gbede zuwa Mopa, a jihar Kogi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel