Faifan murya: Atiku ya bukaci Aaechi da ya dawo PDP kafin zabe

Faifan murya: Atiku ya bukaci Aaechi da ya dawo PDP kafin zabe

- Dan takarar shugaba kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana jawabin fa ministan sufuri, Rotimi Amaechi, akan halin da kasar ke ciki a matsayin kwarin gwiwa

- Atiku ya bukaci darakta janar na kungiyar kamfen din Buhari da yayi murabus daga mukaminsa sannan ya dawo PDP

- Dan takarar shugabancin kasar yace APC da masu mulki a cikinta sun bi hanyoyi daban-daban, inda ya kara da cewa wannan dalilin ne yasa tsaro kasar da lamuran kasar ke ja baya

Dan takarar shugaba kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana jawabin fa ministan sufuri kuma darakta janar na kungiyar kamfen din Buhari, Rotimi Amaechi, akan halin da kasar ke ciki a matsayin kwarin gwiwa, yayinda ya bukace shi da yayi murabus daga mukaminsa sannan ya dawo PDP.

A wani jawabi da ya saki a ranar Litinin, 7 ga watan Janairu, daga kakakinsa, Phrank Shaibu, Atiku yayi korafi akan irin kulawa na musamman da ake ba Amaechi ya fadi gaskiya a wani faifan bidiyo har ta kai an bashi mukamin darakta janar na kamfen din shugaban kasar.

Faifan murya: Atiku ya bukaci Aaechi da ya dawo PDP kafin zabe

Faifan murya: Atiku ya bukaci Aaechi da ya dawo PDP kafin zabe
Source: Depositphotos

Faifan muryar wanda aka alakanta da Ameachi ya nuna rashin imani da gwamnatin APC wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta sannan ya caccaki jihar Lagas a matsayin ‘kauye’.

KU KARANTA KUMA: Kudirin shugabancin Atiku ya hadu da cikas yayinda Buhari ya tarbi yan PDP daga arewa maso gabas

Atiku yace abunda Amaechi ya fadi a faifan muryar yayi daidai da wanda PDP da yan Najeriya ke ji game da halin da al’ummar kasar ke ciki na yunwa sannan akwai bukatar a ceto kasar daga gwamnatin APC a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Atiku yace APC da masu mulki a cikinta sun bi hanyoyi daban-daban, inda ya kara da cewa wannan dalilin ne yasa tsaro kasar da lamuran kasar ke ja baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel