Boko Haram: Jihar Borno ta gabatarwa Buhari manyan bukatu 10

Boko Haram: Jihar Borno ta gabatarwa Buhari manyan bukatu 10

- Wata babbar tawaga daga jihar Borno, ta gabatarwa shugaban kasa Buhari wasu muhimman bukatu 10 na yadda za a bi don kawo karshen Boko Haram a jihar

- An samar da bukatun ne bayan wani taro na masu ruwa da tsaki a harkar tsaro na jihar da ya gudana a birnin Maiduguri

- Gwamnan jihar, Kashim Shettima, ya roki 'yan jaridu, da su boye wadannan bukatu a matsayin sirri, kasancewar sun shafi lamarin tsaro na kasar

Wata babbar tawaga da ta hada da masu rike da sarautun gargajiya, malaman addinai, kungiyoyin mata da na siyasa, karkashin jagorancin gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, a jiya ta gabatarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu muhimman bukatu 10 na yadda za a bi don kawo karshen Boko Haram a jihar.

Gwamna Kashim Shettima, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce bukatun da kuma nazari kan hakan, sun samu ne bayan gudanar da wani babban taro na masu ruwa da tsaki a harkar tsaro na jihar da ya gudana a ranar Litinin din makon da ya gabata a birnin Maiduguri.

Duk da cewa har zuwa yanzu ba a bayyana bukatun da ke kunshe a cikin takardar da suka gabatarwa shugaban kasar ba, rahotanni sun bayyana cewa akwai yiyuwar bayanan sun shafi hanyoyin kawo karshen Boko Haram da ta'addancinsu a fadin jihar.

KARANTA WANNAN: Boko Haram: Har yanzu muna fuskantar hare hare - Shehun Borno ya shaidawa Buhari

Boko Haram: Jihar Borno ta gabatarwa Buhari manyan bukatu 10

Boko Haram: Jihar Borno ta gabatarwa Buhari manyan bukatu 10
Source: Twitter

Tawagar wacce ta kunshi masu rike da sarautun gargajiya, dattawa, mambobin majalisar dokoki dana tarayya, shuwagabannin kananan hukumomi, kuniyoyin mata, kungiyar 'yan jaridu da kungiyoyin kwadago na jihar.

Shettima, a jawabin bude taron, ya ce gaba daya bukatun da nazarin, an lullubesu ne daga sanin jama'a kasancewar sun shafi matsalar tsaron kasar, wanda bayyanasu zai iya kawo cikas ga kudirin da ake yi na kawo karshen ta'addanci a jihar.

Ya ce: "Ranka ya dade, munzo ne da wasu nazarori da kuma bukatu 10, wadanda suke bukatar daukar matakin gaggawa daga fadar shugaban kasa. Wadannan bukatun sun samune bayan wani taron masu ruwa da tsaki kan tsaro da muka gudanar a makon da ya gabata.

"Bayan taron, bamu gaggauta zuwa wajenka ba, munga akwai bukatar mu je Arewacin Borno, mu zanta da wadanda suke zaune a sansanonin gudun hijira da kuma jami'an soji, don samun kwarin guiwan daga garesu.

"Ina rokon 'yan jaridu, da su taimaka su boye wadannan bukatru a matsayin sirri. Bukatu ne akan tsaro, wanda zai zama sirri tsakaninmu da shugaban kasa."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel