Garkuwa da mutane: Tsohon alkali Mamman Nasir ya tsallake rijiya da baya, an sace mai tsaronsa

Garkuwa da mutane: Tsohon alkali Mamman Nasir ya tsallake rijiya da baya, an sace mai tsaronsa

A jiya Litinin ne wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba su kayi yunkurin sace hakimin Malumfashi kuma Galadiman Katsina, Jastis Mamman Nasir.

Rahotanni sun ce tsohon babban alkalin kotun daukaka karar ya tsira amma masu garkuwa da mutanen sunyi awon gaba da hadiminsa mai suna Aminu.

'Yan bindigan sun kai musu hari ne a jiya Litinin misalin karfe 9.30 na dare a tsakanin kauyen Gora da Yammama a titin Dayi-Malumfashi a karamar hukumar Malumfashi na jihar Katsina.

Ya auna arziki

Ya auna arziki
Source: Twitter

An ce 'yan bindigan sun tare hanya ne suna bincika motocci inda suke neman wanda za su sace.

DUBA WANNAN: Fallasa : Dan Boko Haram ya tona asirin yadda suke kai harin bam din Nyanya

An gano cewar basaraken ya fice daga motarsa ya shiga wata motar ne domin kaucewa masu garkuwa da mutanen amma hadiminsa bai fice daga motar da wuri ba kuma suka kama shi su kayi cikin daji dashi tare da wasu matafiya.

Wani mazaunin garin Malumfashi da ya bukaci a sakayya sunansa ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce mutane suna tururuwa zuwa fadar Galadiman domin yi masa jaje.

A cewarsa, daga bisani Jastis Nasir ya bukaci mutane su bashi dama ya huta domin al'amarin ya razana shi.

Anyi kokarin ji ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isa sai dai hakan bai yiwu ba saboda wayarsa na kashe a yayin rubuta wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel