Atiku ya nada Eshanekpe Israel cikin masu yi masa yakin neman zaben 2019

Atiku ya nada Eshanekpe Israel cikin masu yi masa yakin neman zaben 2019

- Wani Mai goyon bayan Shugaba Buhari a da ya koma bangaren Atiku Abubakar

- Eshanekpe Israel zai yi wa Atiku da PDP yakin neman zabe a Yankin Neja-Delta

- Atiku ya nada Israel a matsayin Jagoran Matasan da za su yi masa kamfe a Yankin

Atiku ya nada Eshanekpe Israel cikin masu yi masa yakin neman zaben 2019

Wani babban Masoyin Buhari ya koma goyon bayan Atiku
Source: Depositphotos

Mun ji cewa ‘daya daga cikin wadanda ake tunanin su na goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari a kudancin Najeriya watau Eshanekpe Israel, ya koma goyon bayan ‘dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP watau Atiku Abubakar.

Eshanekpe Israel zai jagoranci yakin neman zaben Atiku Abubakar a Kudu maso kudancin Najeriya bayan PDP ta nada shi a matsayin babban jagoran Matasan da za su yi wa Atiku kamfe a cikin kasar Neja-Delta a zaben 2019.

KU KARANTA: Ayi ta ta kare: Amurka ta shirya baiwa Atiku izinin shiga kasar ta

Kwaitin yakin neman zaben PDP a 2019 ta zabi Israel a matsayin shugaban kungiyar South-South, Youth and Support Groups (SSYSG). Wani babban ‘Dan PDP Sunny Oyewosa yace Matashi zai yi wa Atiku aiki ne a zaben da za ayi.

A baya, an san cewa Eshanekpe Israel, yana goyon bayan gwamnatin Buhari ne. Sai dai wannan mukami da aka ba shi, zai sa yayi wa jam’iyyar PDP aiki a yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur a babban zaben da za ayi bana.

Duk da wannan kamu da Atiku yayi, ita ma jam’iyyar APC tayi nasara wajen samun goyon bayan wasu tsofaffin ‘yan PDP a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya wanda daga nan ne Atiku Abubakar ya fito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel