Kudirin shugabancin Atiku ya hadu da cikas yayinda Buhari ya tarbi yan PDP daga arewa maso gabas

Kudirin shugabancin Atiku ya hadu da cikas yayinda Buhari ya tarbi yan PDP daga arewa maso gabas

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tarbi mambobin jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC

- Bukar Bolori ne ya jagoranci masu sauya shekar daga yankin arewa maso gabas

- Buhari ya gode ma masu sauya shekar kan goyon bayansu da soyayyarsu a gare shi da ma APC

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party daga yankin arewa maso gabas da dama, wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Da yake tarban tawagar yan siyasa daga arewa maso gabas ciki harda masu sauya sheka karkashin jagoranci Bukar Bolori a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 7 ga watan Janairu, shugaba Buhari ya yaba masu akan wannan hukunci da suka yanke sannan yayiwa sabbin mambobin maraba da zauwa APC.

Kudirin shugabancin Atiku ya hadu da cikas yayinda Buhari ya tarbi yan PDP daga arewa maso gabas

Kudirin shugabancin Atiku ya hadu da cikas yayinda Buhari ya tarbi yan PDP daga arewa maso gabas
Source: Depositphotos

Ya ce bai yi mamakin sauya shekar nasu ba saboda mafi akasarin nagartattun mutane da ke arewa maso gabas duk yan APC ne da kuma maso goyon bayan jam’iyyar.

Buhari ya gode ma masu sauya shekar kan goyon bayansu da soyayyarsu a gare shi da ma APC.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar gwamna na PDP a Kano ya sauya sheka zuwa APC

Ya bukace su da kada su yi sanya wajen ganin APC ta yi nasara a zabe mai zuwa.

Bolori, wanda yayi Magana da manema labarai a fadar shugaban kasa yace kasar na bukatar mutum kamar shugaba Buhari domin gyara tattalin arzikinta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel