Dan takarar gwamna na PDP a Kano ya sauya sheka zuwa APC

Dan takarar gwamna na PDP a Kano ya sauya sheka zuwa APC

- Tsohon d an takarar kujerar gwamna a jihar Kano karkashin jam’yyar PDP Injiniya Bello Sani Gwarzo, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

- Gwarzo ya sauya shekar ne tare da da dukkanin magoya bayansa daga kananan hukumomi 44 na jihar

- Hakazalika, kimanin kungiyoyin siyasa 250 a jihar suka hade da kungiyar goyon bayan Buhari domin ganin shugaban kasar yayi nasara a zaben 16 ga watan Fabrairu mai zuwa

Wani dan takarar kujerar gwamna a jihar Kano karkashin jam’yyar Peoples Democratic Party (PDP) Injiniya Bello Sani Gwarzo, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Wadanda suka sauya sheka tare da Gwarzo sun hada da dukkanin magoya bayansa daga kananan hukumomi 44 na jihar.

Hakazalika, kimanin kungiyoyin siyasa 250 a jihar suka hade da kungiyar goyon bayan Buhari domin ganin shugaban kasar yayi nasara a zaben 16 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Dan takarar gwamna na PDP a Kano ya sauya sheka zuwa APC

Dan takarar gwamna na PDP a Kano ya sauya sheka zuwa APC
Source: Depositphotos

A wani kayataccen kwarya-kwarya da aka shirya don tarban masu sauya shekar, sun kaddamar da biyayyarsu da jajircewarsu wajen yin aiki a karkashin kungiyar One 2 Tell 10 Buhari Support Group tare da kudirin tabbatar da nasarar Buhari.

Da yake jawabi a taron, Darakta Janar na kungiyar kamfen din Injiniya Bello Sani Gwarzo, Alhaji Mika’ilu Koki, yace sau uku a jere ubangidan nasu na neman matsayin Gwamna amma sun lura hakarsu bata cimma ruwa don haka suka yanke shawarar komawa APC.

Alhaji Koki yayi korafin cewa tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP bata da niyan magance matsalar talaka suba ga gurbatacciyar mulki irin nata wanda ya hana kasar ci gaba.

KU KARANTA KUMA: An tashi da gawar mutum 3 sannan an samu rauni bayan Magoya-bayan Ganduje sun far ma ‘Yan adawa

Sannan ya kara da cewa kasa da shekaru uku gwamnatin APC karkashin Buhari ta kawo ci gaba sosai da daidaita tattalin arziki, wanda alamu ne na gwamnati mai inganci don haka akwai bukatar yayi tazarce domin ya ci gaba da ayyukan ci gaba da yake kan yi.

Da yake yi masu maraba, Darakta Janar na kungiyar One 2 Tell 10 Buhari Support Group, Dr Abdullahi Baffa Bichi, ya taya masu sauya shekar murna akan wannan yunkuri nasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel