An tashi da gawar mutum 3 sannan an samu rauni bayan Magoya-bayan Ganduje sun far ma ‘Yan adawa

An tashi da gawar mutum 3 sannan an samu rauni bayan Magoya-bayan Ganduje sun far ma ‘Yan adawa

Mun samu labari cewa akalla mutane 3 ne su ka bakunci lahira a lokacin da aka yi wani karo tsakanin Magoya bayan Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma ‘yan adawar sa a jihar Kano.

An tashi da gawar mutum 3 sannan an samu rauni bayan Magoya-bayan Ganduje sun far ma ‘Yan adawa

Mutum 3 sun sheka lahira wajen taron daurin aure a Kano
Source: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto mana cewa wasu Bayin Allah sun rasu inda kuma aka yi wa wasu mutum 2 mummunan rauni a sakamon kicibis da aka yi tsakanin wadanda ke yi wa Gwamnan Kano adawa da kuma Masoyan sa.

Wannan mummunan abu ya faru ne a lokacin da gwamna Abdullahi Ganduje ya leka Garin Dawakin Tofa domin halartar wani daurin aure na ‘yan uwan sa. Rikicin ya fara ne lokacin da wasu su ka fara yi wa mai girma gwamna ihu.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar Ganduje ya lashe zaben Jihar Kano a 2019

Rahoton da mu ka samu jiya shi ne wasu mutanen garin sun fito su na ihun “Bama yi!” ne kurum sai wadansu magoya bayan gwamnan da ke cikin tawagar sa su ka zaro makamai su ka afka masu nan take har su ka kashe mutane 3.

Wani Bawan Allah da abin ya auku a gaban sa ya tabbatar da cewa ya ga gawar mutane 3, sannan kuma yace akwai mutane 2 sa aka yi wa mugun rauni. Yanzu haka wadanda aka yi wa mugun raunin su na kwance su na jinya a asibiti.

Kakakin ‘yan sanda na Kano, Magaji Majiya, ya tabbatar da aukuwar wannan abu. Sai dai jami’an tsaron sun ce mutum guda ne aka kashe sannan kuma wasu na asibiti, inda ya tabbatar cewa za ayi bincike a kuma hukunta masu laifi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel