Idan Buhari ya fitar da sunayen barayin gwamnati, 'yan Najeriya zasu ji kamar su kashe su - Dan majalisa

Idan Buhari ya fitar da sunayen barayin gwamnati, 'yan Najeriya zasu ji kamar su kashe su - Dan majalisa

Dan majalisar tarayya, Mr Ehiozuwa Agbonnayima ya ce hankulan 'yan Najeriya zai matukar tashi game da irin satar kudaden gwamnati da akayi a Najeriya idan Shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da bayannan.

Agbonayima, wadda dan jam'iyyar APC mai mulki ne kuma dan takarar mai wakiltan Ikppha-Okha/Egpr a majalisar ya yi wannan jawabin ne yayin hira da manema labarai ranar Litinin a Benin.

Ya ce 'yan Najeriya za su fusata har ta iya kai ga su nemi kashe wasu daga cikin wadanda suka sace kudin gwamnatin muddin aka saki sunayensu.

Agbonnayima ya ce abin damuwa ne yadda har yanzu 'yan Najeriya basu gane cewa ba Shugaba Buhari bane ya sace kudadensu.

Idan Buhari ya fitar da sunayen barayin gwamnati, 'yan Najeriya zasu kashe su - Dan majalisa

Idan Buhari ya fitar da sunayen barayin gwamnati, 'yan Najeriya zasu kashe su - Dan majalisa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sunaye: Manyan jaruman Kannywood dake cikin kwamitin kamfen din Aisha

Ya ce wadanda ke adawa da tazarcen shugaba Muhammadu Buhari suna adawar ne saboda sun san ba za a sabunta musu lasisin rijiyoyin man fetur dinsu ba idan ya zarce.

Ya yi ikirarin cewa akwai wasu 'yan PDP da ke gwamnatin Buhari da basu son ya yi nasara domin al'umma za su yabawa jam'iyyar APC ne.

Agnonnayima ya ce wani lauyan kasar waje da gwamnatin Najeriya ta dauka aiki ya ce akwai wasu lauyoyin Najeriya da gwamnati ta dauka aiki amma suna yiwa gwamnatin zagon kasa a yunkurin ta na dawo da kudaden da aka sace aka kai kasashen waje.

"Ana gudanar da zabe ne domin cigaba. Idan Buhari ya fitar da sunayen wadanda suka sace kudaden Najeriya, wasu 'yan Najeriya za su so su kashe su.

"Amurka ta bamu cikaken bayanin danyen man fetur da aka sace daga Najeriya.

"Mun gayyaci NNPC kuma sun gabatar mana da hujojinsu. A cikin takardun da suka gabatar, babu wani alama da ke nuna an fitar da danyen man fetur zuwa Amurka.

"Muna da takardun shaida na adadin man da aka fitar, da wadanda suka saya man fetur din da bankunan da akayi amfani da su wajen biyan kudin.

Agbonnayima ya kara da cewa, "Ina jam'iyyar APC ne saboda Buhari ba mai gaskiya ne. Wannan shine dalilin da yasa na ke tare da Buhari," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel