PDP ta sauke babban shugaban ta na Arewacin Najeriya, Gamawa Babayo daga mukamin sa

PDP ta sauke babban shugaban ta na Arewacin Najeriya, Gamawa Babayo daga mukamin sa

- Jam’iyyar PDP ta dakatar da mataimakin shugaban ta na kasa na yankin Arewa

- A jiya PDP ta sauke Sanata Gamawa Babayo daga kujerar sa na wani ‘dan lokaci

- An samu babban jami’in na PDP ne da laifin yi wa jam’iyyar zagon kasa a boye

PDP ta sauke babban shugaban ta na Arewacin Najeriya daga mukamin sa

Majalisar PDP NWC ta cire Babayo Gamawa daga mukamin sa jiya
Source: Facebook

Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta bayyana cewa ta dakatar da daya daga cikin manyan shugabannin ta.Jam’iyyar ta dakatar da Sanata Gamawa Babayo daga mukamin sa ne bayan ta same shi da laifi.

Babban sakataren yada labarai na PDP na kasa baki daya, Kola Ologbondiyan, shi ne ya bada wannan sanarwa a makon nan. Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne bayan bincike.

KU KARANTA: Ana neman PDP ta ruguza kwamitin yakin neman zaben Atiku

A Ranar Asabar din makon da ya gabata watau 5 ga Watan nan ne uwar jam’iyyar ta zauna a Hedikwata da ke babban birnin tarayya Abuja inda ta dauki matakin dakatar da Sanata Gamawa Babayo daga kan kujerar sa.

Kola Ologbondiyan wanda yake magana a madadin jam’iyyar yace an samu shugaban PDP na yankin Arewa watau Babayo Gamawa ne da laifin shiryawa jam’iyyar makarkashiya inda yake aiki da wasu jam’iyyu a boye.

Wannan ya sa jam’iyyar tayi amfani da doka ta dakatar da babban jami’in na ta daga kujerar sa a ranar Litinin. Sashe na 58 na dokar PDP ya haramtawa ‘ya ‘yan PDP hada-kai tare da aiki da sauran jam’iyyu ko ta wani fuska.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel