Shettima da wasu manyan Jihar Borno sun yi taurin kai sun kwana a Munguno

Shettima da wasu manyan Jihar Borno sun yi taurin kai sun kwana a Munguno

Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno ya kwana Garin Munguno domin karfafa gwiwan Bayin Allah da su ka hada da sojoji da ‘yan kato da gora da sauran jami’an tsaro da kuma masu gudun hijira a yankin.

Shettima da wasu manyan Jihar Borno sun yi taurin kai sun kwana a Munguno

Gwamnan Jihar Borno ya kwana a Garin Munguno kwanaki
Source: Facebook

Yanzu haka akwai mutane sama da 57, 000 daga Garuruwa kusan 3 da su ka fake a cikin Garin Munguno. Wannan ya sa gwamnan na Borno ya tsaya ya kwana a cikin Garin a Ranar Juma’ar da ta gabata duk da matsalar tsaro.

Gwamnan ya kwana a cikin Garin na Munguno wanda ke cikin Arewacin jihar Borno ne a kusan daidai lokacin ake fada da ‘yan ta’addan Boko Haram. Idan ba ku manta ba ‘yan ta’addan sun yi yunkurin kawowa Garin hari kwanaki.

Garin Munguno bai wuce kilomita 60 daga Garin Bag aba inda yanzu haka ake gwabzawa tsakanin sojojin Najeriya da Boko Haram. Gwamna Shettima ya tsaya a cikin Garin Monguno ne tun daga Ranar Juma’a har zuwa Asabar da rana.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace daliban jami'a 9 a Jihar Katsina

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Masu ba gwamnan shawara sun yi kokarin ganin ya hakura da kwana a wannan gari bayan ganin irin hare-haren da Boko Haram su ka kai a cikin karamar hukumar Kukawa da kewaye kwanan nan.

Sai dai gwamnan bai ji ta ta su ba, inda ya tashi tare da Sanatan Yankin watau Abubakar Kyari da kuma Farfesa Umara Zulum, wanda yake neman gwamna a APC tare da wasu manyan mukarraban sa domin ganin halin da jama’an sa ke ciki.

Gwamna ya zagaya inda ya shiga barkin Sojoji da ke Garin sannan kuma ya leka wasu makarantu da asibitoci da gwamnatin sa ke ginawa. Daga karshe ya wuce zuwa Gajiginna da Nganzai da Magumeri kafin ya kama hanya ya dawo gida.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel