Jaga-jaga: Yadda 'yan Kwadago ke shirin dagulawa Shugaba Buhari lissafi

Jaga-jaga: Yadda 'yan Kwadago ke shirin dagulawa Shugaba Buhari lissafi

Hadaddiyar kungiyar kwadago a Najeriya, United Labour Congress Of Nigeria, ta ce ta daura damarar gudanar da wani yajin aiki na sai Baba-ta-gani, don matsa lamba ga gwamnatocin kasar su amince da karin albashi mafi karanci na naira dubu talatin.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta BBC, kungiyar ta umarci 'ya'yanta a duk fadin Nijeriya su tashi da haramar fara wannan yajin aiki tun a tsakar daren jiya, da kuma wata gagarumar zanga-zanga da za a yi a duk fadin kasar.

Jaga-jaga: Yadda 'yan Kwadago ke shirin dagulawa Shugaba Buhari lissafi

Jaga-jaga: Yadda 'yan Kwadago ke shirin dagulawa Shugaba Buhari lissafi
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Amurka na shirin baiwa Atiku 'biza'

Legit.ng Hausa ta samu cewa, wannan l'amarin daiu na zuwa ne da nufin nuna rashin gamsuwa da matakin gwamnatin kasar a kan mafi karancin albashi.

Sakataren tsare-tsare na hadaddiyar kungiyar kwadago ta ''ULCN'', Kwamadred Nasir Kabiru Ahmad kuma jagoran zanga-zangar ta ranar Talata, ya ce sun umarci duk 'ya'yansu su zauna a gida, wadanda suka fito kuma za su "zunduma zanga-zanga a duk fadin kasar".

Ya ce kugiyoyin kwadagon kasar sun dauki wannan mataki ne saboda gazawar shugaban kasa na mika kudurin dokar biyan mafi karancin albashi ga zauren majalisun Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel