Zaben 2019: Wasu Yarbawa sun kaso jirgin yaudarar Shugaba Buhari akan Tinubu

Zaben 2019: Wasu Yarbawa sun kaso jirgin yaudarar Shugaba Buhari akan Tinubu

Kungiyar nan da ba ta gwamnati ba dake ikirarin kare muradun 'yan kabilar Yarbawa a tarayyar Najeriya watau Afenifere sun bayyana alakar da ke tsakanin shugaba Buhari da kuma jigo a cikin jam'iyyar APC, Cif Bola Tinubu da yaudara tsantsa.

Shugaban kungiyar ta Afenifere, Yinka Odumakin ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da wakilin majiyar mu inda ya ce matsayin jagoran gangamin yakin neman zaben da Shugaba Buharin ya ba Tinubu ba zai haifar da da mai ido ba.

Zaben 2019: Wasu Yarbawa sun kaso jirgin yaudarar Shugaba Buhari akan Tinubu

Zaben 2019: Wasu Yarbawa sun kaso jirgin yaudarar Shugaba Buhari akan Tinubu
Source: Facebook

KU KARANTA: Diyar David Mark ta kunyata shi a garin su

Legit.ng Hausa ta samu cewa har ila yau a cewar shi Mista Odumakin, wai shugaba Buhari yayi hakan ne kawai domin ya kaucewa halartar muhawarar da aka shirya masa shi da sauran yan takarkarin kujerar shugabancin kasar.

Sai dai kuma shugaban na kungiyar Afenifere ya kara da ba shugaba Buhari shawarar da ya gaggauta canja tunanin sa game da halartar muhawarar domin kuwa idan bai je ba to fa lallai hakan zai iya ja masa matsala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel