Faifen Amaechi: Atiku yayi kira ga Buhari ya hakura da takara a 2019

Faifen Amaechi: Atiku yayi kira ga Buhari ya hakura da takara a 2019

Babban abokin hamayyar shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019, watau Atiku Abubakar, ya tofa albarkacin bakin sa game da faifen da ke yawon inda aka ji Rotimi Amaechi yana tir da gwamnatin Buhari.

Faifen Amaechi: Atiku yayi kira ga Buhari ya hakura da takara a 2019

Da wuya samu wanda zai kashe Najeriya irin Buhari - Atiku
Source: Facebook

Atiku Abubakar, wanda yake harin kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya bayyana cewa zaben Buhari a bana zai jefa Najeriya cikin wani hali na masifar wahala ne bayan jama’a sun ji abin da Ministan sufurin kasar yake fada.

Atiku yayi wannan jawabi ne ta bakin wani hadimin sa a kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu. Shuaibu ya nemi Buhari ya hakura, ya janye takarar sa a zaben na bana. A cewar sa, hakan zai sa a gujewa asarar kudi a banza a kasar.

KU KARANTA: Mai dakin Atiku ta bayyana abin da zai faru idan ya zama shugaban kasa

Hadimin ‘dan takaran na PDP yake cewa Mai dakin shugaban kasar watau Hajiya Aisha Buhari, tayi gaskiya lokacin da tace wasu mutane ne dabam ke jan ragamar mulkin Najeriya a madadin Mijin na ta da dinbin jama’a su ka zaba a 2015.

Shuaibu yake cewa bayanin da aka ji Rotimi Amaechi, wanda shi ne Darektan yakin neman zaben Buhari tun 2015 yana yi, ya tabbatar da cewa gwamnati mai-ci ta gaza ta kowane fuska. 'Dan takaran yace faifen da aka fallasa ya isa aya.

Tolu Ogunlesi, wanda yana cikin masu ba shugaban kasa shawara yayi kokarin nuna cewa an dauki wannan faifai ne tun 2014 a lokacin mulkin PDP. Sai dai daga baya kuma yace wasu ne su kayi amfani da siddabaru don kurum sukar Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel