Zan kawo karshen ware kunshin kudin tsaro a Kano - Abba K. Yusif

Zan kawo karshen ware kunshin kudin tsaro a Kano - Abba K. Yusif

Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Kabir Yusuf, ya ce batun ware kunshin wasu kudi da gwamnoni ke yi da sunan harkar tsaro zai zama tarihi a jihar Kano idan aka zabe shi gwamna.

Ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Kano yayin jawabi ga manema labarai a wurin biki taya shi murnar cika shekaru 56 da magoya bayansa suka shirya.

Dan takarar na PDP ya yi zargin cewa ware makudan kudaden da sunan tsaro, wata hanya ce ta waske wa da kudin al'umma.

Zan kawo karshen ware kunshin kudin tsaro a Kano - Abba K. Yusif

Zan kawo karshen ware kunshin kudin tsaro a Kano - Abba K. Yusif
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace wani basarake a jihar Katsina

"Kowa ya san cewar kunshin kudin tsaro da ake magana wata hanya ce ta karkatar da makudan kudade ba tare da tsoron tuhuma ba.

"Kudin na tafiya ne aljihun wasu zilamammun mutane kalilan da ba zasu taba koshi da cin kudin jama'a ba," a cewar Abba.

A cewar sa, idan aka zabe shi gwamna a jihar Kano, zai yi amfani da kudaden ta hanya mafi dacewa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar kunshin kudin tsaro wani kudi mai yawa da gwamnati ke bawa jihohin kasar nan domin amfani da su a sha'anin tsaro.

Biliyoyi ne masu yawa da suka banbanta daga jiha zuwa jiha da kason su ya dogara a kan ma'aunin kalubalen tsaro da jiha ke da shi.

Mallam Nura Ma'aji, shugaban wadanda suka shirya taron, ya ce sun yi ne don taya Abba murnar cika shekaru 56 cikin koshin lafiya.

Kazalika ya bayyana cewar taron manuniya ce ga masu nuna cewar PDP ba zata cin zaben gwamna a jihar Kano ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel