Sanatocin da suka tsaya wa Nnamdi Kanu sun kasa biyan N100m ta kariya bayan ya tsere

Sanatocin da suka tsaya wa Nnamdi Kanu sun kasa biyan N100m ta kariya bayan ya tsere

- Nnamdi Kanu ya tsere daga Najeriya

- Ya bar wadanda suka tsaya masa a kotu da kajaga

- Sun kasa biyan kudin da kotu ta gindaya

Sanatocin da suka tsaya wa Nnamdi Kanu sun kasa biyan N100m ta kariya bayan ya tsere

Sanatocin da suka tsaya wa Nnamdi Kanu sun kasa biyan N100m ta kariya bayan ya tsere
Source: Facebook

Bayan da aka kame Nnamdi Kanu tun a 2015, aka kuma sako shi a 2017, ya zamo dan rajin kafa kasar Bayafara ta kabilar Ibo, sojoji sun neme shi sun rasa, inda shi kuma ya bullo bayan shekara guda a kasar Israila, inda yake neman mafaka.

Dan tawayen ya aiko da sako inda yae bada hakuri kan guduwar tasa, yace babu yadda zayyi ne saboda kashe shi ake neman yi a lokacin.

Kafin a sako shi dai, Sanatoci uku ne suka tsaya masa da cewa zai bar batun siyasa, sannan zai dena tsoma baki kan lamarin rabewar Najeriya, sharudda da duk ya karya.

DUBA WANNAN: Yawan Ayyukan na bashi da Kasar China keyi A Afirka, Najeriya ce ta daya

Bayan dawowar Buhari daga rashin lafiya, sai ya aika sojoji su kamo shi, amma suka neme shi suka rasa, ya gudu.

A yanzu kam, su Sanatocin ke tsaka da kotu, inda kotun ta tilasta musu biyan kudi ko suyi asarar kadarorinsu da suka ajje wa kotu, kudin ya kai N100m.

Sanata Abaribe, maimakon biyan kudin, ya shigar da kara kotu, inda yake neman kotu ta cire wannan takunkumi, bisa batun cewa ba laifin su bane yaron ya tsere.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel