Da dumin sa: An cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya

Da dumin sa: An cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace ta cimma yarjejeniya tsakanin ta da kungiyar malaman jami'o'in karar nan watau Academic Staff Union of Universities (ASUU) a turance da yanzu haka ke yajin aiki tun watan Nuwambar da ya gabata.

Ministan Kwadago na gwamnatin tarayyar ne dai Dakta Chris Ngige ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala wata tattaunawa da kungiyar malaman jami'o'in da yammacin ranar Litinin a garin Abuja.

Da dumin sa: An cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya

Da dumin sa: An cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya
Source: UGC

KU KARANTA: Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta samu cewa Mista Ngige ya bayyana cewa tuni bangarorin biyu suka cimma yarjejeniya a tsakanin su kuma gwamnatin tarayya ta amince da sakin wasu kudade da malaman jami'o'in ke bin su da suka kai Naira biliyan 15.4.

Shi kuwa a nasa bangaren, shugaban kungiyar malaman ta ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi cewa yayi tabbas sun cimma yarjejeniya akan wasu abubuwa a tsakanin su da gwamnatin amma za su koma wajen mambobin su domin tattaunawa akan batun.

Ana sa ran dai daga yanzu a kowane lokaci kungiyar ta ASUU zata iya janye yajin aikin nata da take yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel