Amaechi yayi magana game da faifan muryar sa da aka nada yana sukar Buhari

Amaechi yayi magana game da faifan muryar sa da aka nada yana sukar Buhari

Babban Ministan sufuri kuma daraktan gangamin yakin neman zaben shugaba Buhari na wannan shekarar ta 2019, Mista Rotimi Amaechi yayi magana game da faifan muryar sa da aka nada yana sukar Buhari a sirrance.

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya bayyana cewa shi dai a iya sanin sa bai da labarin wannan sautin muryar kuma baya da wata alaka da shi don ba shi ne yayi shi ba.

Amaechi yayi magana game da faifan muryar sa da aka nada yana sukar Buhari

Amaechi yayi magana game da faifan muryar sa da aka nada yana sukar Buhari
Source: UGC

KU KARANTA: Wasu mafusatan matasa sun kona motar kamfe din Saraki a Kwara

Mai karatu dai zai iya tuna cewa mun kawo maku labarain yadda a wani faifai da aka dauka bai sani ba, Amaechi yana cewa "Lallai ana fama da talauci a wannan kasar, babu mai jin dadi kwatata, ba Manoma ba, ‘yan siyasar ma ba dadi suke ji ba sannan su kansu dalibai kuka suke.

Kowa na kuka saboda rashin samun walwala yadda ya kamata.

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa cikin wannan faifai an ji Amaechi na cewa ”Shi fa Buhari ba ya daukar shawarar kowa abinda yake so ya ke yi, sannan babu abin da ya sha masa kai.

Za ka iya rubuta duk abinda kake so abinka bai damu ba, domin ba karatu yake yi ba ma. Idan ma yaga ana sukar sa sai ya kira ka yace zo, zo ka gani wai zagi na suke yi, sai ya fashe da dariya abin sa.

Phrank Shuaibu, na kamfen din Atiku ne ya fidda wannan faifai da minista Amaechi ya zazzaro wadannan zantuka.

Phrank ya kara da cewa hakan ya dada tabbatar da irin kalaman da maidakin shugaban Kasa, Aisha Buhari ta rika cewa maigidanta ba shine ke gudanar da mulkin Najeriya ba, cewa wasu mutane ne da basu wuce uku ba suke yadda suka ga dama a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel