Za'a shiga yajin aiki ba tare da an sake baiwa gwamnati kashedi ba - Kwadago

Za'a shiga yajin aiki ba tare da an sake baiwa gwamnati kashedi ba - Kwadago

- Kungiyar kwadago zata fara yajin aiki

- A yau ne kungiyar da kawayent su keyin zanga zanga a fadin kasar nan

- Rashin mika rahoton kwamiti akan karin karancin albashi ga mahukunta ne dalili

Za'a shiga yajin aiki ba tare da an sake baiwa gwamnati notice ba - Kwadago

Za'a shiga yajin aiki ba tare da an sake baiwa gwamnati notice ba - Kwadago
Source: UGC

A shirye shiryen yajin aikin da za'ayi a fadin kasar nan akan tabbatar da 30,000 karancin albashi, wanda kungiyar kwadago ke shiryawa, a yau ana zanga zanga don tirsasa gwamnati akan tayi abinda ya dace.

Yan kungiyar kwadago na jihar Oyo sunyi zanga zanga a ranar laraba inda suka zagaye babban birnin jihar, Ibadan.

Kungiyar tace "Kungiyar kwadago bazata bada tabbacin kwanciyar hankali da zaman lafiya na ma'aikatu matukar aka wuce 31 ya watan Disamba, 2018 ba tare da an mika bukatar ta ga majalisar dattawa ba."

DUBA WANNAN: An fara amfani da sunan EFCC ana yaudarar mutane, EFCCn ta dauki sabbin matakai

Shugaban ULC, Joe Ajaero, yace duk da ba a sa ranar fara yajin aikin ba, zamu iya fara yajin aikin ko washegarin da muka gama zanga zangar lumana.

Yace: "Zamu iya farawa yau ko ma gobe. A taron da mukayi mun amince da cewa 31 ga Disamba, 2018 zamu koma yajin aiki matukar ba a mika bukatar mu ga mahukuntan ba. Abinda muke nufi shine zamu fara yajin aikin a kowacce rana bayan nan. Yau, gobe ko jibi ba tare da mun sanar da gwamnati ba."

Sakataren NLC, Dr. Peter Ozo-Eson, yace, a jiya, kungiyoyin kwadago na jihohi 36 na fadin kasar nan da duk wata kungiya dake karkashin ta ko kawance da ita dasu fita zanga zanga.

"Gobe rana ce ta zanga zanga."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel